An Yi babban Rashi: Fitaccen Ɗan Kasuwa a Kano, Alhaji Aminu Ɗantata Ya Rasu

An Yi babban Rashi: Fitaccen Ɗan Kasuwa a Kano, Alhaji Aminu Ɗantata Ya Rasu

  • Fitaccen ɗan kasuwar Kano, Alhaji Aminu Ɗantata, ya rasu a daren ranar Juma'a, 27 ga Yuni, 2025, yana da shekaru 94 a duniya
  • Ɗantata ya rasu ne a Abu Dhabi, babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a cewar ɗaya daga cikin makusantansa Sanusi Dantata
  • Tsohon mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya ce Kano da Najeriya sun yi babban rashin dattijo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rahotanni da muke samu yanzu na nuni da cewa Allah ya karbi rayuwar fitaccen ɗan kasuwar Kano, Alhaji Aminu Ɗantata.

An sanar da rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwar ne a safiyar ranar Asabar, kuma an ce ya rasu ne a daren ranar 27 ga Yuni, 2027.

An samu labarin rasuwar hamshakin dan kasuwar Kano, Alhaji Aminu Dantata
Fitaccen dan kasuwar Kano, marigayi Alhaji Alhaji Aminu Dantata. Hoto: @SasDantata/X
Source: Twitter

Ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu

Gidan rediyon Premier FM da ke Kano ne ya sanar da rasuwar a shafinsa na Facebook, duk da cewa bai bayar da ƙarin bayani a kai ba.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Muhammadu Sanusi II da Aminu Bayero za su haɗu a birnin Madina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta fahimci cewa Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu ne yana da shekaru kusan 94, kuma ya bar ƴaƴa da jikoki masu yawa.

Rahotanni sun bayyana cewa za a sanar da lokacin jana'izarsa zuwa anjima, yayin da ake neman al'umma sun sanya shi a cikin addu'o'insu.

"Kano ta rasa daya daga cikin 'ya'yanta" - Bashir

Bashir Ahmad, tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatar da rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata a shafinsa na X.

A cikin sakon da ya aika, Bashir Ahmad ya ce:

"Kano ta rasa daya daga cikin manyan 'ya'yanta, yayin da Najeriya ta yi rashin babban mai fada aji, watau Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
"Ya kasance gamji maza abin koyi, mai yawan taimako, ga kuma yakana. Za a ci gaba da tunawa da gudunmawarsa a ci gaban tattalin arzikin kasa da bunkasa rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kwara ya fusata, ya gurfanar da tsohon ɗan majalisa da ɗan uwansa a kotu

"Muna rokon Allah ya gafarta masa zunubansa, ya yi masa sakayya da gidan Aljannatul Firdausi."
An rahoto cewa Alhaji Aminu Dantata ya rasu ne a Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa.
Fitaccen dan kasuwar Kano, marigayi Alhaji Alhaji Aminu Dantata. Hoto: @SasDantata/X
Source: UGC

Alhaji Aminu Dantata ya rasu a Abu Dhabi

Hamshaƙin attajirin na Nijeriya Alhaji Aminu Dantata ya rasu ne a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a cewar ɗaya daga cikin makusantansa Sanusi Dantata.

Sanusi Dantata ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Hakika, daga Allah muke kuma gare shi ne za mu koma.
"Don Allah, ku sanya Alhaji Aminu Dantata a cikin addu'o'inku, wanda ya rasu 'yan awanni da suka wuce a Abu Dhabi.
"Shi ne ɗa ɗaya tilo da ya yi saura a cikin 'ya'yan Alhassan Dantata.
"Allah ya gafarta masa, ya kuma sanya shi a cikin Aljannatul Firdausi, Amin."

Aikin alherin Dantata ga al'umma

Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun attajirai da masu taimakon al’umma a tarihin Najeriya.

Ba wai kawai mashahurin ɗan kasuwa bane ba, mutum ne da ya sadaukar da wani ɓangare mai yawa na rayuwarsa wajen taimakon al’umma, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya da addini.

Kara karanta wannan

An ɗage jana'izar fitaccen ɗan kasuwa, Aminu Ɗantata saboda ƴar matsala a Madina

Ɗantata ya kafa gidauniyoyi da dama da ke bayar da tallafi ga ɗalibai masu karatun gaba da sakandire da na jami’a, ciki har da ɗaliban da ke karatu a kasashen waje.

Ya gina makarantu, masallatai da asibitoci a sassan Kano da ma wasu jihohin Arewa, domin tallafa wa mabukata da rage radadin rayuwa.

Tasirin Dantata ga matasan Najeriya

Baya ga taimako kai tsaye, Aminu Ɗantata ya kasance mai ba da shawara ga matasa masu tasowa a harkar kasuwanci da shugabanci.

An dade ana girmama shi a matsayin dattijo mai hangen nesa, wanda ke bai wa mutane dama, ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.

Rayuwarsa ta sadaukarwa da jin ƙai ta sa ya kasance ginshiki a cikin al’umma, kuma al’umma za su ci gaba da tunawa da irin gudunmawar da ya bayar har abada.

Dantata ya tallafawa Borno da N1bn

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Borno ta sake samun karin tallafi domin kara karfin gwiwa wajen taimaka wa wadanda ambaliya ta shafa a Maiduguri.

A wannan lokaci, fitaccen attajiri kuma dattijo, Alhaji Aminu Dantata, ne ya bayar da tallafi na Naira biliyan 1.5 domin taimakawa al’ummar da abin ya shafa.

Ambaliyar da ta faru kwanakin baya ta jawo asarar rayuka da dama tare da shafar kusan mutane miliyan biyu, wanda ya sa Dantata ya kai dauki da kudi masu tsoka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com