Tsaurin Ido: An Cafke Matasa 4 kan Zargin Gagarumar Sata a Majalisar Tarayya
- Jami'an tsaron Majalisa a birnin Abuja sun damke matasa hudu da suka shiga sata a cikin ginin na majalisar da safiyar yau Juma'a 27 ga watan Yunin 2025
- An kama su ne da sassafe lokacin da suka dawo domin ɗaukar sauran abin da suka sata makon da ya gabata daga wurin
- An mika su ga 'yan sanda don bincike da yiwuwar gurfanarwa duba da irin barna da suka tafka dalilin satar a wurin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an tsaro sun kama wasu matasa kan zargin sata a majalisar tarayya da ke Abuja.
Akalla matasa hudu ne aka kama a safiyar ranar Juma’a bisa zargin sace manyan wayoyin lantarki a majalisar wanda aka ce yana da matukar tsada.

Source: Twitter
An kama masu laifin ne da sassafe ta hannun jami’an tsaron majalisar, inda aka tsare su a ofishin SPU, cewar rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Abuja ke fama da matsalolin tsaro
Wannan na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 da kama wani da ake kira Sajan dan sanda a babban filin ajiye mota a gaban fadar shugaban ƙasa.
Wasu ma’aikata sun bayyana cewa Sajan ɗin ya taɓa aiki a Majalisar Tarayya kafin a tura shi zuwa wani wurin daban domin ci gaba da bincike saboda a gano gaskiyar lamarin.
Birnin Abuja dai na fama da matsaloli kama daga na yan bindiga zuwa barayi da kuma masu kwace waya wanda ya zama ruwan dare.
Gwamnatin tarayya ta sha yin alkawarin kawo karshen matsalar amma har yanzu abin ya ƙi ci, ya ki cinyewa wanda ke kara jefa fargaba a zukatan jama'a.

Source: Original
Dubun matasa ya cika garin sata a majalisa
An ce matasan sun fara sace wani ɓangare na wayar lantarki ne tun makon jiya, kafin su dawo ranar Juma’a domin ɗaukar sauran da ke wurin.
Sai dai a wannan karon sun ci karo da jami’an tsaro, lamarin da ya jawo kamasu da kuma mika su ga hukuma don ci gaba da bincike.
A cewar majiyoyi, an mika waɗanda ake zargi da satar wayar lantarkin zuwa hannun ‘yan sanda don bincike da yiwuwar gurfanarwa.
A tuna cewa wata mota mallakin ma’aikacin majalisa da aka sace a Oktobar shekarar 2024 har yanzu ba a samo ta ba bayan shigar da kai kara.
Yan sanda sun musanta sace mutane a Abuja
A baya, mun ba ku labarin cewa an yi ta yaɗa wasu rahotanni a kafafen sada zumunta masu cewa an sace mutane kusan 200 kan hanyar Ƙaduna zuwa Abuja.
Sai dai Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta fito fili ta musanta rahotannin inda ta bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a cikin labaran inda ta bukaci mutane su yi watsi da shi.
Hakazalika ta ƙara da cewa an kwashi shekara biyu ba tare da samun rahoton yin garkuwa da mutane ba a kan hanyar da ake magana kanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

