NAHCON Ta Samu Tsaiko a Jigilar Alhazan Najeriya zuwa Gida, Za Su Ƙara Zama a Saudiyya
- Hukumar Hajji ta Ƙasa watau NAHCON ta ɗage ranar kammala jigilar mahajjatan Najeriya daga ƙasar Saudiyya zuwa gida
- NAHCON ta ce an samu tsaiko ne sakamakon cunkoson jiragen da ake samu a filayen Saudiyya saboda kowace ƙasa na ƙoƙarin kwashe alhazanta
- A halin yanzu, ana sa ran kammala kwaso alhazan Najeriya zuwa gida a ranar 2 ga watan Yuli, maimakon 28 ga watan Yuni da aka tsara tun farko
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da ƙarin wa’adin kammala jigilar Mahajjatan Najeriya na 2025 zuwa gida daga ƙasar Saudiyya.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mataimakiyar darakta kuma mai magana da yawun hukumar NAHCON ta ƙasa, Fatima Usara, ta fitar a ranar Alhamis.

Source: Twitter
Hukumar ta ce ba za a iya kammala jigilar mahajjatan zuwa gida a ranar 28 ga Yuni kamar yadda aka tsara tun da farko ba, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan
Kotu ta yi hukunci kan bukatar Firaministan Isra'ila bayan kammala yaƙi da ƙasar Iran
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NAHCON ta ɗaga ranar gama kwaso mahajjata
"Lokaci ya ƙure, aikin dawo da mahajjata gida sai ya kai har zuwa ranar Talata, 2 ga Yuli, 2025, idan babu wani cikas da ya taso daga baya,” in ji ta.
Fatima Usara ta kuma bayyana yawan mahajjatan da suka rage, da adadin sawun da kamfanoni jiragen sama za su yi kafin kamma dawo da ƴan Najeriya gida.
Adadin mahajjatan Najeriya da suka rage a Saudiyya
"Kamfanin Max Air na da ragowar mahajjata 6,019 da zai kwaso zuwa gida, kuma yana amfani da jirage biyu masu kujeru 560, wato jimillar kujeru 1,120 a rana.
"Sai kuma UMZA Aviation Services, yana da ragowar mahajjata 4,850, shi ma dai jirage biyu gare shi waɗanda ke iya ɗauko mutum 796 a rana.
"FlyNas, yana da mahajjata 2,480 da zai dawo da su gida, kamfanin na da ƙarfin ɗauko fasinjoji 819 a kullum. Na karshe, Air Peace, wanda ke daga ragowar mahajjata 1,635 da zai kwaso zuwa Najeriya."
- Fatima Usara.

Source: Twitter
Meyasa aka samu jinkirin kwaso alhazan Najeriya?
NAHCON ta roƙi mahajjatan Najeriya da har yanzu suke a Saudiyya da su yi haƙuri da jinkirin da aka sanu wajen dawo da su gida.
Hukumar ta bayyana cewa cunkosom jiragen sama daga ƙasashen duniya ne ya haddasa wannan jinkirin, rahoton The Cable.
“Don Allah a lura cewa ƙarancin jigilar jirage da ake gani a yanzu wajen dawo da mahajjata gida yana da nasaba da cunkoson zirga-zirgar jirage da ke faruwa a ƙasar Saudiyya bayan gama aikin Hajj."
“A wannan lokaci ne ƙasashe da dama ke ƙoƙarin kwashe 'yan ƙasarsu zuwa gida, kuma hakan na haifar da cunkoso a filayen jiragen saman Saudiyya," im ji Fatima.
Jihohi 11 sun tallafawa alhazai a Saudiyya
A wani labarin, kun ji cewa mahajjatan Najeriya daga jihohi 11 sun samu tallafi daga gwamnoninsu yayin da suke gudanar da aikin Hajjin bana a Saudiyya.
Ana lissafin cewa jihohin guda 11 sun ba da tallafin N6.2bn domin sauƙaƙawa Alhazan yayin da suke zaune a ƙasa mai tsarki.
Wannan dai na ɗaya daga cikin taimakon da gwamnonin jihohi suka yi wa mahajjatansu, domin tabbatar da walwala da jin daɗinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
