An Ware Kwana 3 domin Zaman Makokin Kashe Zaratan Sojojin Najeriya 17

An Ware Kwana 3 domin Zaman Makokin Kashe Zaratan Sojojin Najeriya 17

  • Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana kwanaki uku na jimami domin girmama sojoji 17 da suka mutu a wani mummunan hari a Jihar Neja.
  • An kai harin ne a Kwana Dutse, inda ‘yan bindiga suka kai farmaki kan sansanin soji a Neja da Kaduna.
  • An umarci dukkan hafsoshi da cibiyoyin soja a fadin ƙasar nan da su rinka kasa-kasa da tutar soji yayin da ake cikin lokacin jimamin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar dakarunta 17 a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai musu a yankin Kwana Dutse da ke ƙaramar hukumar Mariga, Jihar Neja

Rahotanni sun nuna cewa harin ya girgiza ƙasa baki daya, tare da haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban Fulani a Kogi, sun harbi iyalan shi da AK47

Za a yi kwana 3 ana jimamin sojoji 17 da aka kashe
Za a yi kwana 3 ana jimamin sojoji 17 da aka kashe. Hoto: HQ Nigeria Army
Source: Facebook

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa sojojin sun bayyana cewa an ware daga ranar 25 zuwa 27 ga Yuni, 2025 a matsayin kwanakin jimami.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar sojin ta bayyana cewa an ware kwanakin ne domin girmama rayuwar dakarun da suka sadaukar da kansu don kare ƙasa.

Yadda aka kai hari sansanonin sojojin Najeriya

Sanarwar ta bayyana cewa hare-haren sun auku ne a sansanonin soji biyu da ke jihohin Neja da Kaduna, inda ‘yan bindigar suka kai farmaki tare da hallaka dakarun.

A lokacin jimamin, an umarci dukkan cibiyoyin soja da hafsoshi a fadin Najeriya da su yi kasa da tutarsu a matsayin alamar jimami da karrama wadanda suka mutu a bakin aiki.

Sojoji za su ci gaba da girmama jami'ansu

Rundunar sojin ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin hanyoyin da ke nuna yadda take daraja rayuwar dakarunta.

Punch ta wallafa cewa rundunar ta addada cewa sojojin da suka rasa rayukansu za su ci gaba da kasancewa cikin tarihin bajinta da kishin ƙasa.

Kara karanta wannan

An harbe dan bindiga, Mai Jakka da yake wa 'yan Najeriya barazana a TikTok

Sanarwar ta kuma bayyana ta’aziyyar rundunar ga iyalan da abokan arzikin dakarun da suka mutu, tana mai cewa ana cikin shiri domin tallafawa iyalan da suka rasa masoyansu.

An yaba da sadaukarwar sojojin Najeriya

Kwanakin jimamin da aka ware za su zama lokacin nazari ga al’umma dangane da irin sadaukarwar da sojoji ke yi domin kare Najeriya.

Wannan harin ya sake jaddada muhimmancin tsaro da rawar da dakarun soji ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.

Sojojin Najeriya yayin aiki a wani daji
Sojojin Najeriya yayin aiki a wani daji. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Yayin da ake cikin lokacin juyayi, masana sun jaddada muhimmancin tallafawa dakarun soji da iyalan da suka rasa ‘yan uwansu, tare da yabawa matakin rundunar soji na nuna jarumta.

Sojoji sun bayyana cewa za su ci gaba da aiki da ƙwazo da kishin ƙasa, duk da barazana da hare-haren da suke fuskanta daga ‘yan ta’adda a sassan ƙasar.

An kashe dan bindiga Mai Jakka a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sa-kai sun yi nasarar hallaka dan bindiga Mai Jakka a jihar Zamfara.

Rahotannin da Legit ta samu sun nuna cewa an kashe jagoran 'yan bindigan ne a wata arangama tare da wani abokin shi.

Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yaba da kokarin da aka yi wajen kashe babban dan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng