Daruruwan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Sansanin 'Yan Sanda, An Yi Barna

Daruruwan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Sansanin 'Yan Sanda, An Yi Barna

  • Wasu gungun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki a wani sansanin ƴan sanda da ke jihar Kebbi
  • Ƴan bindigan waɗanda yawansu ya kai fiye da mutum 300 sun yi awon gaba da makamai bayan sun fafata da jami'an da ke bakin aiki
  • Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma sun bi sahun 'yan bindigan domin ƙwato makaman da suka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Fiye da ƴan bindiga 300 ɗauke da muggan makamai sun farmaki ƙauyen Makuku da ke cikin ƙaramar hukumar Sakaba a jihar Kebbi.

Ƴan bindigan sun kai hari ne kan sansanin ƴan sanda tare da yin awon gaba da bindigu ƙirar AK-47 guda takwas a ranar Alhamis.

'Yan bindiga sun farmaki sansanin 'yan sanda
'Yan bindiga sun kwashe makamai a sansanin 'yan sanda a Kebbi Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da basarake a jihar Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindigan suka kai harin

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa ƴan bindiga masu ɗauke da makamai, da ake zargin masu satar shanu ne, suna tafiya ne tare da tarin dabbobin da suka sace daga jihar Neja kan hanyarsu ta zuwa Zamfara.

Ƴan bindigan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Alhamis kamar yadda aka samu labari.

A cewar majiyoyin, harin ya janyo musayar wuta mai tsanani tsakanin jami’an tsaro da ƴan bindigan.

Duk da haka, ƴan bindigan sun yi rinjaye a kan jami’an da ke bakin aiki a lokacin. A yayin harin, ƴan bindigan sun ƙona motar aikin ƴan sanda ƙirar Toyota Hilux, sannan suka ƙwace bindigu AK-47 guda takwas.

Bayan faruwar lamarin, dakarun sojojin rundunar Operation Fansan Yanma tare da wasu jami’an tsaro daga sassa daban-daban sun hanzarta zuwa yankin da abin ya faru domin gudanar da ayyukan ceto da dawo da makaman da aka sace.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki kauyukan Sokoto, an samu asarar rayuka

Dakarun Sojoji sun kai ɗauki

Dakarun sojojin na bin sahun ƴan bindigan ta hanyoyin da suka bi domin tserewa, tare da himmatuwa wajen kamo su da kuma dawo da dabbobin da suka sato daga jihar Neja.

'Yan bindiga sun yi barna a Kebbi
'Yan bindiga sun farmaki sansanin 'yan sanda a Kebbi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Har yanzu ba a bayyana adadin waɗanda suka jikkata ko rasa rayukansu ba a lokacin musayar wutar, amma harin ya jefa mazauna yankin cikin firgici da fargaba.

Rahotanni sun bayyana cewa jama’a da dama sun fara barin yankin domin tsira da rayukansu, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da sintiri a dazuka da hanyoyin da ke da alaƙa da wurin domin ganin an dawo da doka da oda.

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, SP Abubakar Nafiu, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa bai da cikakkun bayanai kan harin amma zai bincika kafin ya ba da bayanai.

"Eh yanzu ba ni da cikakkun bayanai kan lamarin, amma zan bincika sai na kira ka daga baya."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Jami'an DSS sun cafke rikakkun 'yan bindiga bayan dawowa daga Saudiyya

- SP Abubakar Nafiu

Sai dai, bai yi hakan ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan bindiga sun sace shugaban Fulani

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani shugaban Fulani a jihar Kogi da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Ƴan bindigan sun sace shugaban Fulanin ne bayan sun kai hari a wani sansanin makiyaya da ke ƙaramar hukumar Lokoja.

A yayin harin da ƴan bindigan suka kai, sun harbi matarsa da ɗansa Abdulsalam a hannu da ƙafa, inda su biyun ke ci gaba da yin jinya a asibitin Ashafa da ke kusa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng