An Harbe Dan Bindiga, Mai Jakka da Yake wa 'Yan Najeriya Barazana a TikTok

An Harbe Dan Bindiga, Mai Jakka da Yake wa 'Yan Najeriya Barazana a TikTok

  • Wasu rahotanni sun bayyana cewa an kashe dan bindiga Mai Jakka a wani hari da ‘yan sa-kai suka kai a garin Garaji, kusa da hanyar Gusau-Sokoto a jihar Zamfara
  • Mutane sun yi farin ciki da mutuwar Mai Jakka da ya shahara wajen yada bidiyon tashin hankali da zagin gwamnati da isgilanci wa al'umma a TikTok
  • Duk da yawaitar rahotanni kan mutuwar shi, har yanzu babu karin bayani daga hukumomin tsaro ko gwamnatin jihar Zamfara kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An ruwaito cewa an kashe shahararren dan bindiga, Mai Jakka, wanda ake kira da Kacalla Mai Jakka, a wani farmaki da ‘yan sa-kai suka kai.

Wasu rahotanni sun nuna cewa a ranar 25 ga Yuni, 2025 ya mutu a yankin Mayanchi da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Kotu ta kawo karshen shari'ar Mama Boko Haram da wasu mutum 2 kan damfarar N11m

An harbe dan bindiga Mai Jakka a Zamfara
An harbe dan bindiga Mai Jakka a Zamfara. Hoto: Bashir Ahmad|Zagazola Makama
Source: Facebook

Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad na cikin wadanda suka tabbatar da labarin mutuwar dan ta'addan a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe shi tare da wani abokin aikinsa a wata arangama da ta auku a kusa da kauyen Garaji da ke kan hanyar Gusau zuwa Sokoto.

Yadda Mai Jakka ya shahara a TikTok

Mai Jakka ya kasance sananne a kafar TikTok, inda yake wallafa bidiyo na yada tsoro, durkusar da jami’an tsaro, da kuma nuna irin barnar da yake yi wa al’umma.

Ana zargin yana amfani da kafar wajen jan hankalin matasa da kuma amfani da ita wajen tsokanar gwamnati da al’umma.

Wasu daga cikin bidiyonsa sun nuna yadda yake raba kuɗi da kayayyaki ga mabiyansa, yana mai yin hakan da gangan don zubar da mutuncin hukumomi.

Daily Post ta wallafa cewa mutanensa sun addabi kauyuka da dama a Zamfara, inda suka yi garkuwa da mutane, kashe manoma da kuma ƙona gidaje da gonaki.

Kara karanta wannan

Za a kafa dokar kisa ga masu taimakon 'yan bindiga a Kebbi

Martanin jama’a kan kisan Mai Jakka

Daya daga cikin wadanda suka yi martani game da kisan akwai mai taimaka wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad.

A cikin wani saƙo da ya wallafa, Bashir ya ce:

“Mun yi korafi sosai game da wannan mugun mai suna Mai Jakka, wanda ya rika amfani da TikTok wajen wulakanta gwamnati da al’umma.
"Yanzu muna murna da rahoton da ke nuna cewa an kawar da shi ta hannun jaruman ‘yan sa-kai a jihar Zamfara.
"Wannan nasara ce ga iyalan wadanda ya kashe da kuma nasara ga zaman lafiya da adalci.”
Hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad
Hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad. Hoto: Aso Villa
Source: Twitter

Ko da yake rahotanni daga jama’a da masu fafutuka sun tabbatar da kisan, har yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar Zamfara ko kuma rundunar ‘yan sanda da sojoji.

'Yan bindiga sun sace basarake a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun sace wani basarake a Bauchi.

Kara karanta wannan

An kashe yaran Sheikh Ibrahim Khalil a Benue, gwamnan Kano ya yi magana mai zafi

Rahotanni da Legit Hausa ta samu sun tabbatar da cewa an sace basaraken ne a karamar hukumar Ganjuwa.

Biyo bayan faruwar lamarin, rahotanni sun bayyana cewa jami'an 'yan sanda sun bazama cikin daji domin ceto basaraken.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng