Majalisar Dokokin Taraba Ta Tsage Gaskiya kan Zargin Shirin Tsige Mataimakin Gwamna

Majalisar Dokokin Taraba Ta Tsage Gaskiya kan Zargin Shirin Tsige Mataimakin Gwamna

  • Majalisar dokokin jihar Taraba ta fito ta yi magana kan zargin tana shirin tsige mataimakin gwamna, Alhaji Aminu Alkali.
  • Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikin jita-jitar
  • Hon. Nelson Len ya ba da tabbacin cewa mataimakin gwamnan yana jinya ne shiyasa ba ya gudanar da ayyukansa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Majalisar dokokin jihar Taraba ta yi magana kan jitar-jitar shirin sauke mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Aminu Alkali.

Majalisar dokokin ta ƙaryata jita-jitar shirin sauke Alhaji Aminu Alkali, wanda yanzu haka ke karɓar magani a wani asibiti da ke Abuja.

Majalisar dokokin Taraba ta yi karin haske kan shirin tsige mataimakin gwamna
Majalisar dokokin jihar Taraba ta ce babu shirin tsige mataimakin gwamna Hoto: @Agbukefas
Source: Facebook

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Hon. Nelson Len, ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai a Jalingo a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi magana kan zama abokin takarar Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu shirin tsige mataimakin gwamnan Taraba

Hon. Nelson Len ya ce babu wani shiri ko tunani da majalisar ke yi na sauke ko sauya mataimakin gwamnan daga muƙaminsa.

Shugaban kwamitin yaɗa labaran ya bayyana cewa ana sa ran Aminu Alkali zai koma bakin aikinsa bayan ya kammala samun sauki gaba ɗaya, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Ya roƙi jama’a da su yi watsi da jita-jitar cewa majalisar na shirin ayyana cewa ba zai iya ƙara gudanar da aiki ba.

Haka kuma ya jaddada cewa babu ɗaya daga cikin rassan gwamnati uku a jihar da ya fara wani tsari na neman cire ko sauya mataimakin gwamnan daga muƙaminsa.

"Mataimakin gwamna, Alhaji Aminu Alkali, yana jinya a wani asibiti da ke Abuja, kuma yana samun sauƙi. Zai koma bakin aiki da zarar ya warke gaba ɗaya daga jinyar da ya daɗe yana yi."
"Yana buƙatar lokaci don ya murmure sosai domin ya iya gudanar da ayyukan da suka shafi rayuwarsa da na gwamnati."

Kara karanta wannan

Mataimaki a 2027: Barau ya fadi shirinsa kan yin aiki da Shugaba Tinubu

“Babu wani yunkuri daga kowanne ɓangare na gwamnati, ko majalisa, ko bangaren shari’a ko na zartaswa, na ganin an maye gurbin Mataimakin gwamna."
"Abin da ake mayar da hankali a kai shi ne yadda za a tabbatar ya warke ya kuma koma bakin aiki."

- Hon. Nelson Len

Babu shirin sauya mataimakin gwamnan jihsr Taraba
Majalisar dokokin Taraba ta musanta shirin tsige mataimakin gwamnan Taraba Hoto: Legit.ng
Source: Original

An buƙaci jama'a su yi watsi da jita-jitar

Ya kuma buƙaci jama’ar jihar da su yi watsi da duk wata jita-jita da ke cewa majalisar dokokin tana shirin ayyana cewa Alkali ba zai iya ci gaba da aiki ba.

Mataimakin gwamnan dai ya fara hutu na jinya tun daga watan Nuwamba 2024, abin da ya haifar da damuwa a zuƙatan wasu mutanen jihar dangane da tsawon lokacin da ya dauka ba tare da komawa bakin aiki ba.

Gwamnatin Taraba ta musanta naɗa mataimakin gwamna

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Taraba ta musanta cewa ta naɗa sabon mataimakin gwamna.

Kwamishiniyar yaɗa labarai ta jihar ta bayyana cewa ba a naɗa mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar, Hamman-Adama Adamu a muƙamin ba.

Hajiya Zainab ta ba da tabbacin cewa har yanzu Alhaji Aminu Alkali shi ne mataimakin gwamnan jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng