"Bai Taba ba": Tsohon Hadimin Tinubu Ya Sake Yin Fallasa kan Shugaban Kasa

"Bai Taba ba": Tsohon Hadimin Tinubu Ya Sake Yin Fallasa kan Shugaban Kasa

  • Tsohon hadimin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna takaicinsa kan yadda aka riƙa fifita wasu mutane fiye da shi
  • Aliyu Audu ya bayyana cewa a kusan shekara biyu da ya yi yana aiki a ƙarƙashin Shugaba Tinubu, bai samu damar zama domin tattaunawa da shi ba
  • Hakazalika ya sake nanata ƙudirinsa na ganin cewa mai girma Bola Tinubu ya yi bankwana da kujerar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mai taimakawa Shugaba Bola Tinubu kan harkokin harkokin jama'a, Aliyu Audu, ya sake jaddada aniyarsa ta yin aiki don kifar da shugaban ƙasa a 2027.

Aliyu Audu ya sake jaddada matsayarsa ta yin aiki tuƙuru domin ganin Shugaba Tinubu bai sake lashe zaɓe ba a shekarar 2027.

Tsohon hadimin Tinubu ya caccake shi
Aliyu Audu ya ce ba su zama da Shugaba Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Jagoran na ƙungiyar APC Rebirth Movement ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin wata hira da ya yi a shirin 'Prime Time' na tashar Arise tv.

Kara karanta wannan

Mataimaki a 2027: Barau ya fadi shirinsa kan yin aiki da Shugaba Tinubu

Aliyu Audu wanda kwanan nan ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu, ya bayyana cewa duk da kasancewarsa a matsayin mai magana da yawun shugaban ƙasa, bai samu damar ganawa da shi kai tsaye ba har tsawon kusan shekaru biyu.

Tsohon hadimi ya soki Bola Tinubu

Tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasan ya soki Tinubu saboda ba wa shahararren mawakin Afrobeat, David Adeleke (wanda aka fi sani da Davido), da kuma ɗan siyasar Legas, Abdul-Azeez Olajide Adediran (Jandor), damar ganawa da shi.

Ya nuna takaicin cewa shi da kansa da yake aiki a ƙarƙashin shugaban ƙasan bai taɓa samun irin wannan dama ba.

“Na yi aiki wa shugaban ƙasa har kusan shekaru biyu. Ban taɓa samun zama da shi ba. Ina ɗaya ne daga cikin masu magana da yawunsa."
"Amma ya zauna da Davido, wanda ya zage shi 'yan makonni kafin nan. Sannan ya zauna da Jandor, wanda ma bai zo na biyu ba a zaben Legas. Hakan bai da wata ma’ana."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi magana kai tsaye kan Atiku da El Rufai masu shirin kifar da shi a 2027

- Aliyu Audu

Aliyu Audu ya soki Bola Tinubu
Aliyu Audu ya soki Tinubu kan ganawa da Davido Hoto: @DOlusegun
Source: Getty Images

Ƴan adawa na ganawa da Tinubu

Idan ba a manta ba kwana biyar kafin Aliyu Audu ya yi murabus, Shugaba Tinubu ya karɓi baƙuncin Davido da kawunsa, Gwamna Ademola Adeleke, a gidansa da ke Ikoyi, Legas.

Haka kuma a watan Maris da ya gabata, Jandor, wanda ya tsaya takarar gwamna a Legas a zaɓen 2023 ƙarƙashin PDP, ya gana da Shugaban ƙasa bayan ficewarsa daga jam’iyyar.

Shugaba Tinubu ya magantu kan ƴan haɗaka

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan yunƙurin da manyan ƴan adawa suke yi na kafa haɗaka.

Mai girma Bola Tinubu ya bayyana ƴan siyasar da ke jagorantar haɗskar a matsayin ƴan gudun hijira na siyasa waɗanda suke neman farfaɗowa.

Shugaban ƙasan ya buƙaci magoya bayansa da su yi fatali da yunƙurin da ƴan siyasan suke yi na ganin cewa sun kifar da shi a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng