'Ban da Talakawa': Gwamnatin Tinubu Ta Kwantarwa Jama'a Hankali kan Dokar Haraji

'Ban da Talakawa': Gwamnatin Tinubu Ta Kwantarwa Jama'a Hankali kan Dokar Haraji

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da cewa waɗanda ke samun ƙasa da N250,000 a wata ba za su biya haraji ba daga 2026
  • Shugaban kwamitin sauya tsarin haraji, Taiwo Oyedele, ya ce dokar ba za ta cire kuɗi daga aljihun talakawa ba, za ta kare su
  • Oyedele ya ce gwamnatin na kokarin rage gibin da ke cikin tara haraji, kuma sun ware masu ƙasa da N250,000 a matsayin matalauta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Bayan rattaba hannu kan sabon kudirin haraji a Najeriya, an fayyace yadda dokar za ta kasance.

Gwamnatin Bola Tinubu ta ce mutanen Najeriya da ke samun ƙasa da N250,000 a wata ba za su biya harajin kuɗin shiga ba.

An fadi wadanda za su ke biyan sabon haraji
Gwamnatin Tinubu ta kwantarwa jama'a hankali kan dokar haraji. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

An fadi wadanda za su biya haraji

Jagoran Kwamitin Shugaban Kasa kan Tsarin Haraji, Taiwo Oyedele shi ya bayyana hakan a shirin Politics Today na Channels TV.

Kara karanta wannan

NLC ta fusata, ta shirya yamutsa gwamnati a 'yan kwanaki masu zuwa

Oyedele ya bayyana haka ne bayan Tinubu ya amince da dokokin haraji a yau Alhamis 26 ga watan Yunin 2025.

Ya ce yanzu gidajen da ke samun ƙasa da N250,000 a wata za a ɗauke su a matsayin matalauta a tsarin gwamnati.

Oyedele wanda aka naɗa a watan Yuli 2023, ya bayyana wa'adinsa na shekara biyu da ya jagoranta a matsayin mai cike da ƙalubale da nasarori.

Ya ce dokokin za su fara aiki daga Janairu 2026, kuma ba su da niyyar ƙara haraji sai dai ƙarfafa tattalin arziki da gano masu kaucewa.

Ya ƙara da cewa dokokin za su kare kasuwanci da tabbatar da gwamnati ba ta ɗaukar haraji daga matalauta ba, suna da niyyar kawo ci gaba.

Ya ce:

“Wannan dokar haraji ba za ta ba ka kuɗi a hannu ba, amma aƙalla ba za ta ɗauke kuɗinka ba idan kai talaka ne.”
Tinubu ya rattaba hannu kan dokokin haraji
Gwamnatin Tinubu fadi wadanda dokokin haraji zai shafa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Yawan adadin kudin da zai sanya biyan haraji

Kara karanta wannan

'Har gida muka cin masa': Gwamnatin Zamfara ta faɗi illar da ta yi wa Bello Turji

Oyedele ya ce babu wanda ke samun ƙasa da wannan adadi da zai biya haraji saboda ma ba su da isasshen kuɗi don rayuwa mai sauƙi.

“Mun cire haraji daga matakin ƙasa, mun rage wa masu matsakaici, sai kuma mun ɗan ƙara wa masu samun kuɗi da yawa.
“Matsakaicin mutum mai samun kusan N1.8 zuwa N2m a wata zai ci gaba da biyan haraji, amma an rage masa yawan da ake karɓa.”

- Cewar Ayodele

Ya bayyana cewa waɗanda ke cikin wannan rukuni na matsakaici suna wakiltar kusan kashi 5% na yawan al’ummar Najeriya, cewar Punch.

Oyedele ya ce kwamitinsu ya tattauna sosai akan layin talauci a Najeriya don sanin wanda bai kamata a ɗora masa haraji ba.

Tinubu ya ƙi sanya hannu a kudirin NDLEA

Kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya ƙi sanya hannu kan ƙudirin dokar NDLEA saboda ya saɓa wa wasu dokoki.

An ce wannan shi ne karo na biyu a wannan makon da Tinubu ya ƙi amincewa da sanya hannu kan kudiri, saboda rashin daidaitonsu da doka.

Duk da haka, Tinubu ya sanya hannu kan sababbin kudirorin gyaran haraji huɗu da za su kawo sauyi a tattalin arzikin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.