NLC Ta Fusata, Ta Shirya Yamutsa Gwamnati a 'Yan Kwanaki Masu Zuwa

NLC Ta Fusata, Ta Shirya Yamutsa Gwamnati a 'Yan Kwanaki Masu Zuwa

  • Kungiyar kwadago ta NLC ta ce za ta rufe babban birnin tarayya, Abuja bayan Shugaba Bola Tinubu ya gama kaddamar da ayyuka
  • Wannan ya biyo bayan watanni da ma’aikatan Abuja suka suna yajin aiki saboda rashin biyan hkkokinsu yadda ya dace
  • Kungiyar ta fayyace cewa ko a baya, sai da NKC ta ba gwamnati wa’adin kwanaki bakwai kafin ta tsunduma yajin aiki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT, Abuja – Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ya ce tana shirin rufe Abuja bayan Shugaba Bola Tinubu ya kammala kaddamar da ayyukan ci gaba da aka tsara ran 3 ga Yuli 2025.

Shugaban kungiyar a Abuja, Dr Stephen Knabayi, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, inda ya ce ma’aikata ke fushi da gwamnati.

Kara karanta wannan

Haraji: Nyesom Wike ya fadi manyan Abuja da ke jawo masa matsala

Kungiyar kwadago da Bola Tinubu
Gwamnatin Abuja ta fusata NLC Hoto: Bayo Onanuga|Nigeria Labour Congress - HQ
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Dr Knabayi ya ce su na fatan matakin zai jawo hankalin hukumomi domin su warware matsalar yajin aikin da ma’aikatan kananan hukumomi ke yi.

Ma'aikatan gwamnati na yajin aiki a Abuja

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko a Abuja da malamai a makarantun Abuja na yajin aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma an rufe ofisoshin kananan hukumomi shida na yankin, su na ci gaba da zama babu ma’aikata tsawon watanni.

Malamai da sauran ma’aikatan kananan hukumomi sun shiga yajin aiki saboda rashin biyan mafi karancin albashi da kuma rashin biyan karin alawus dinsu.

NLC ta yi kaca-kaca da gwamnati

Shugaban NLC, Dr Knabayi, wanda ya ce wannan hali da cewa "abin takaici ne matuka", ya ce shugabannin kananan hukumomin sun bar kungiyar ba tare da wata mafita ba illa ta rufe birnin Ya ce kungiyar ta bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga gwamnatin Abuja a ranar 13 ga Yuni don ta biya bukatun malamai, ma’aikatan lafiya da sauran ma’aikatan kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

2027: Barau ya yi magana bayan an nemi Tinubu ya ajiye Shettima ya dauke shi

Ministan Abuja, Nyesom Wike
NLC na shirin tsunduma yajin aiki a Abuja Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Facebook

Ya bayyana cewa wannan wa’adin na da nasaba da matsayar da shugabannin hadin gwiwar kungiyoyin NUT da NULGE da kuma kungiyar ma’aikatan lafiya suka cimma.

Shugaban ya ce NLC ta dakata da daukar mataki ne domin ba Shugaba Bola Tinubu damar kammala kaddamar da ayyuka a Abuja a wani bangare na cika shekaru biyu a mulki.

Ya bayyana takaici a kan yadda hukumomin suka rufe idanunsu, yayin da ma'aikata ke galabaita a birnin.

NLC ta yiwa Tinubu wankin babban bargo

A baya, mun wallafa cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta soki gwamnatin Bola Tinubu, tana mai cewa shekaru biyu da ya shafe a kan karagar mulki babu dadi.

Shugaban ƙungiyar, Kwamared Joe Ajaero, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar kan halin da ma'aikatan kasar nan ke ciki a mulkin jam'iyyar APC.

A cewarsa, maimakon sauƙin rayuwa da Tinubu ya ɗauko alƙawarin kawowa, ‘yan Najeriya sun tsinci kansu cikin fargaba da hauhawar farashi da ke jefa su a wahala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng