Tinubu Ya Kunyata Majalisar Tarayya, Ya Ƙi Sanya Hannu a Ƙudurin Dokar NDLEA
- Shugaba Bola Tinubu ya ƙi sanya hannu kan ƙudirin dokar NDLEA saboda ya saɓa wa wasu dokokin rarraba kuɗi na gwamnati
- Wannan shi ne karo na biyu a wannan makon da Tinubu ya ƙi amincewa da sanya hannu kan kudiri, saboda rashin daidaitonsu da doka
- Duk da haka, ana sa ran Tinubu zai sanya hannu kan sababbin kudirorin gyaran haraji huɗu da za su kawo sauyi a tattalin arzikin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ƙi sanya hannu a kan sabon kudirin dokar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA Bill, 2025).
An bayyana matsayar shugaban ƙasar ne a cikin wata wasiƙa da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya ki amince wa da kudurin NDLEA
Kudirin dokar yana neman bai wa NDLEA ikon riƙe wani kaso na kuɗaɗen da aka samu daga laifuffukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma Shugaba Tinubu ya ce wannan mataki ya saɓa wa dokokin kuɗi da ake amfani da su a halin yanzu.
A cikin wasiƙar Tinubu, ya bayyana cewa a ƙarƙashin tsarin da ake bi yanzu, "Ana saka duk kuɗaɗen da aka samu daga aikata laifuffuka a cikin asusun gwamnati na mallakar kadarorin da aka kwace."
Ya ƙara da cewa:
"Za a iya raba kuɗaɗe ga kowace hukumar da ke da alhakin kwato kadarori, ciki har da NDLEA, ne kawai ta hanyar amincewar shugaban ƙasa, bayan samun izinin majalisar zartarwa ta tarayya da majalisar dokoki ta kasa."
Tinubu ya ce tsarin da ake bi a halin yanzu yana tabbatar da riƙon amana da kuma sa ido kan kudaden da aka kwato, don haka babu buƙatar canza shi.
Sau 2 Tinubu na kin amincewa da kudirori
Kin amincewa da kudirin NLEA a ranar Alhamis shine karo na biyu a wannan makon da Shugaba Tinubu ya ƙi sanya hannu a kan wani kudiri.
Tun a ranar Talata, ya ƙi amincewa da kudirin dokar gidauniyar dakin karatu ta majalisar dokoki ta kasa ta 2025.
Shugaba Tinubu ya ce ya ki sanya hannu kan kudurorin ne saboda rashin daidaito da manufofin dokokin tarayya, musamman game da samar da kuɗi ga hukumomi, haraji, da tsarin albashi.

Source: Twitter
Tinubu zai sa hannu kan dokokin haraji 4
Duk da haka, ana sa ran zai sanya hannu kan sababbin kudirorin gyara haraji guda huɗu, waɗanda za su kawo sauyi a tsarin kuɗi da tattalin arziki na Najeriya.
Kudirorin guda huɗu su ne: Kudirin haraji na Najeriya, kudirin dudanar da haraji na Najeriya, kudirin kafa hukumar haraji ta Najeriya, da kudirin kafa hukumar haɗin gwiwar haraji.
Majalisar tarayya ta amince da kudurorin gyaran harajin ne bayan shawarwari masu zurfi da aka yi da ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki daban-daban.
Wani dan majalisa daga Enugu ya koma APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani ɗan majalisar wakilai, Chimaobi Atu, daga jihar Enugu, ya koma jam'iyyar APC mai mulki daga jam'iyyar LP a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya yi magana kai tsaye kan Atiku da El Rufai masu shirin kifar da shi a 2027
Hon. Chimaobi Atu ya bayyana rikicin shugabanci a cikin LP a matsayin dalilin da ya sa ya bar jam'iyyar zuwa APC.
Sauya sheƙarsa ya zo kwanaki biyu bayan Peter Akpanke, daga Cross River, Paul Nnamchi daga jihar Enugu, suka sauya sheka daga Jam'iyyar Labour zuwa APC.
Asali: Legit.ng

