An Nemi Kudaden da Aka Ƙwato Daga Hannun Barayin Ƙasa a CBN an Rasa, Sun Yi Ɓatan Dabo
- Rahotanni sun bayyana cewa kudaden da aka kwato daga hannun barayin kasa tsakanin 2016 zuwa 2019 sun yi batan dabo a bankin CBN
- Kungiyar kare hakkokin tattalin arziki ta SERAP ta bayyana hakan a shafinta na X, @SERAPNigeria
- Kungiyar masu fafutukar ta kara da cewa an umarci babban bankin kasar da ya yi bayanin yadda aka yi kudaden har suka bata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Kungiyar kare hakkokin tattalin arziki ta SERAP ta ce ta gano cewa kudaden da aka kwato daga hannun barayin kasa tsakanin 2016 da 2019 na an kuma sace su a babban bankin Najeriya (CBN).
SERAP ta ce babban mai binciken kudi na tarayya, Shaakaa Kanyitor Chira, ya umarci CBN da ta yi bayanin yadda aka yi kudaden suka bata.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X (wanda aka fi sani da Twitter) @SERAPNigeria, a ranar Laraba, 14 ga Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An samu rahoton cewa an kudade da aka kwato a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2019 sun yi batan dabo a hannun babban bankin Najeriya (CBN)."
- A cewar SERAP.
'Yan Najeriya sun mayar da martani
@DavinJavin
Watakila Mikiya ce ta tashi da kudin a wannan karon
@realadnantweet
Ban san inda za mu dosa a kasar nan ba.
Cin hanci da rashawa a Najeriya ya kai makin da ba a iya misaltawa.
@Knot73211261
Wannan ko a masarautar dabbobi hakan ba zai iya faruwa ba, ko da kuwa ba su da cikakkiyar hikima kamar mutane….!!!
@akpudje_efepete
Lamarin yadda 'yan siyasa suka koma yin yahoo yahoo ya zama wani abu dabam, 'yan sanda da DSS ba za su bi diddigin su ba, sai zaluntar 'yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba kawai suka iya.
Karanta sanarwar a kasa:
Asali: Legit.ng