1447: Jihohin Najeriya da Suka Ayyana Hutu saboda Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci
Yau, Alhamis ya kama 1 ga watan Muharram na shekarar 1447 na hijirar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama daga Makkah zuwa Madinah, na nufin shigowar sabuwar shekara.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Duk da al’ummar Musulmin duniya na bikin sabuwar shekarar Musulunci ta 1447 bayan Hijira a wannan rana, ba ranar hutu ba ce a tarayyar Najeriya.

Source: Facebook
Legit ta tattaro cewa, kamar yadda kalanda na Miladiyya ke da watanni 12, haka ma ta Hijiriyya, sai dai akwai bambanci a kwanakin.
Adadin ranakun kalandar Musulunci ya fi ƙaranci, domin yana da kimanin ranaku 354 zuwa 355, sabanin kalanda na Mikadiy da ke da ranaku 365 ko 366.
1. Shekarar 1447: Gwamnatin Kano ta ba da hutu
Gwamna Abba Kabir Yusuf na daga cikin jerin gwamnonin Najeriya da suka ayyana ranar hutu don bikin sabuwar shekarar Musulunci ta 1447AH. Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya wallafa sanarwar a shafinsa na Facebook.

Source: Facebook
Sanarwar ta ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya shawarci Musulmi da su duba ayyukansu na shekarar da ta gabata, tare da daura damarar inganta su a 1447.
Ya kuma nemi a dage da yiwa ƙasa addu'a, musamman domin samun dorewar zaman lafiya, samun wadatar arziki da ci Gaba mai dore wa.
2. Kwara ta ba da hutun shekarar Musulunci
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara ya taya Musulmin jihar murna bisa shigowar sabuwar shekarar Hijira ta 1447.
Gwamnan ya amince da ranar Alhamis, 26 ga Yuni – wato ranar farko ta watan Muharram – a matsayin hutu ga ma'aikatan jihar.

Source: Facebook
Sanarwar da gwamnati ta fitar ta ce:
"Hijira na koyar da sadaukarwa da ta haɗin gwiwa don al’amura su inganta, da kuma barin duk wani abu da ke sabawa zaman lafiya, daidaito, da adalci a cikin al’umma."
3. Gwamnatin Oyo ta ba Musulmi hutun sabuwar shekara
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana ranar Juma’a, 27 ga Yuni a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin bikin shigowar sabuwar shekarar Hijira ta 1447AH.
Sanarwar hutun na kunshe ne cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Olanike Adeyemo, ya fitar a ranar Laraba, 25 ga Yuni.

Source: Facebook
A cikin sanarwar, gwamnan Seyi Makinde ya ce:
Gwamnan ya bukaci kowa da kowa da ya yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar, da ƙasar baki ɗaya gaba ɗaya.
A cewar sanarwar, ranar hutun aiki ta shafi dukkanin ma’aikatu da ofisoshin gwamnati a faɗin jihar.
4. An ba da hutun shekarar Musulunci a Katsina
Gwamna Dikko Radda na Katsina ya taya Musulmi mazauna jihar da sauran sassan duniya murnar sake ganin sabuwar shekarar addinin Musulunci.
A sanarwar da gwamnati ta fitar, ta ce:
“Ina taya ‘yan’uwa Musulmi murna a wannan gagarumin lokaci na sabuwar shekarar Musulunci. Hijira wata babbar alama ce a tarihin Musulunci, wadda ke tunatar da mu irin sadaukarwa, juriyar Annabi (SAW)."
Gwamna Radda ya bukaci al’umma da su dauki darussa daga Hijira ta hanyar inganta hadin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da kabilu daban-daban.
5. Gwamnatin Zamfara ta bi sahun wasu jihohi
Gwamna Lawal ya taya al’ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekarar Hijira, tare da kira ga daukacin mazauna Zamfara da su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’in zaman lafiya.
Sanarwar da Kwamishinan yada labarai da al'adu na jihar, Hon. Mahmud Muhammad Dantawasa ya fitar ta ce:
“Mai girma gwamna yana mika gaisuwar taya murna ga al’ummar Musulmi, kuma yana ƙarfafa gwiwar jama’a da su ci gaba da yin addu’o’i domin dawo da zaman lafiya, cigaba da daidaito a jihar Zamfara da Najeriya gaba ɗaya—musamman ganin yadda matsalolin tsaro ke ci gaba da addabar sassa daban-daban."
shekara a Musulunci' Inji Malami
Malamin addinin Musulunci a Kano, Malam Yunus Shu'aib Alkanawee ya bayyana Al-Muharram da daga daga cikin watanni masu falala.
Ya bayyana cewa:
"Watan Al-Muharram, daya ne daga cikin watannin masu alfarma a Musulunci. Akwai watan Dhul Hijja, akwai Dhul Ƙada, sai kuma watan Muharram, sai kuma wata na hudueahi ne watan Rajab."
"Ba shakka a wannan watan, yana da kyau a gabatar da ibada a ciki, kamar abin da ya shafi azumi , tara ga wannan wata da kuma 10 ga wannan wata, kamar yadda ya zo a Sunna ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama."
Ya gargadi Musulmi a kan bukukuwa a wannan wata, ganin cewa ya saba da koyarwar addinin Musulunci.
Ya shawarci Musulmi da su yawaita neman gafarar Allah Subhanahu Wata'ala a kan kurda-kurdar da su ka gabata,, su kara da zumunci da kara yawaita alheri.
Malamin Musulunci ya magantu kan zaben 2027
A baya, mun wallafa cewa Shugaban majalisar malamai ta Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi zargin ana son Bola Tinubu da Kashim Shettima.
Malamin ya yi barazanar cewa ba zai sake goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 ba, idan har shugaban kasar ya cire Kashim Shettima daga matsayin mataimakinsa.
Fitaccen malamin ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu da ya kira "marasa kishin kasa" ke ƙoƙarin haddasa husuma a tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



