Tsohon Gwamna, Bafarawa Ya Ziyarci IBB bayan Kafa Sabuwar Kungiyar Arewa

Tsohon Gwamna, Bafarawa Ya Ziyarci IBB bayan Kafa Sabuwar Kungiyar Arewa

  • Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, ya ce Arewa na bukatar muryoyi masu ƙarfi da za su tsaya su kare muradunta
  • Ya bayyana hakan ne lokacin da kungiyar Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative ta kai masa ziyara a Minna
  • Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce an kafa wannan ƙungiya ne domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban Arewa da Najeriya baki ɗaya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce Arewa na bukatar fitattun mutane masu kishin yankin.

Janar Ibrahim Babangida (Mai ritaya) ya ce akwai bukatar muryoyi da za su riƙa bayyana bukatun al’umma da kare muradunsu cikin gaskiya da rikon amana.

Kara karanta wannan

2027: Barau ya yi magana bayan an nemi Tinubu ya ajiye Shettima ya dauke shi

Bafarawa ya ziyarci IBB a Minna na jihar Neja
Bafarawa ya ziyarci IBB a Minna na jihar Neja. Hoto: Bayo Onanuga|Ahmad Imran Muhammad
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa IBB ya bayyana haka ne a yayin ziyarar da shugabannin kungiyar Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative suka kai masa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yaba da kafa ƙungiyar, inda ya ce lokaci ya yi da Arewa ke bukatar irin wannan ƙungiya da manyan mutane kamar Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa da Dr Abdullahi Idris ke jagoranta.

Za a kaddamar sabuwar kungiyar Arewa

A jawabin da shugaban kwamitin amintattun ƙungiyar, Attahiru Bafarawa, ya ce kafa ƙungiyar wata dama ce da za ta ba Arewa murya da karfi a harkokin siyasa da mulki a Najeriya.

Ya bayyana cewa za a ƙaddamar da ƙungiyar a hukumance a ranar 10 ga Yuli, 2025, a garin Kaduna, inda ya roki tsohon shugaban da ya ba da goyon bayansa da fatan alheri.

Da yake magana da manema labarai bayan ganawarsu da IBB, Bafarawa ya ce Najeriya da Arewa na cikin wani hali na bukatar zaman lafiya da gaskiya a mulki.

Kara karanta wannan

'Ka hakura da takara': Baba Ahmed ya fadawa Atiku abin da ya kamata ya yi a 2027

Leadership ta wallafa cewa Attahiru Bafarawa ya jaddada cewa ba daidai ba ne a riƙa zargin wani yanki da laifin koma bayan ƙasa.

Bafarwa ya ce ana bukatar hadin kai a Najeriya
Bafarwa ya ce ana bukatar hadin kai a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Tsohon gwamnan Sokoto, Bafarawa ya ƙara da cewa:

“Na zo ne domin na ga lafiyar shugaba IBB kuma mu nemi shawararsa a kan halin da ƙasa ke ciki da yadda za a inganta ta.
"Babu wata ƙasa da za ta cigaba sai an samu zaman lafiya da fahimta tsakanin jama’a.”

Ya bayyana shi cewa ba dan jam’iyyar APC ba ne, ba dan PDP ba ne, kuma bai shiga wata ƙungiya ta siyasa ba, yana tafiyar da siyasar sa ne ta hanyar da za ta kawo cigaba da fahimta.

Dalilin kafa kungiyar Arewa Cohesion

A nasa jawabin, Darakta Janar na ƙungiyar, Dr Abdullahi Idris, ya bayyana cewa burin ƙungiyar shi ne haɗin kai da cigaban yankin Arewa.

Ya ce lokaci ya yi da Arewa za ta tsaya da kanta cikin martaba da jagoranci mai ma’ana domin ci gaban yankin da ƙasa baki ɗaya.

Bafarwa ya yi magana kan sauya sheka

Kara karanta wannan

ADA: Atiku ya gana da 'yan Kanyywood, 'yan siyasar Arewa kan sabuwar tafiya

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa ya yi magana yayin da 'yan siyasa ke tururuwar shiga jam'iyyar APC.

Attahiru Bafarawa ya ce yawancin 'yan siyasa suna komawa APC ne domin muradun kansu ba domin talaka ba.

A yanzu haka dai 'yan majalisun tarayya da dama sun koma APC yayin da ake da sauran lokaci kafin zaben 2027 ya kankama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng