'Tinubu na Mayar da Najeriya Kamar Lagos': Sarkin Lafiya Ya Faɗi Abin da Ya Gani a Ikko

'Tinubu na Mayar da Najeriya Kamar Lagos': Sarkin Lafiya Ya Faɗi Abin da Ya Gani a Ikko

  • Sarkin Lafia, kuma Alkalin Kotun Koli mai ritaya, Sidi Bage, ya ce shugabancin Bola Tinubu yana sauya Najeriya kamar yadda ya sauya Legas
  • Ya bayyana hakan ne lokacin da Shugaba Tinubu ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa dake Lafia, jihar Nasarawa ranar Laraba
  • Tinubu ya gode masa, ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan albarkatu, noma, da gyaran tituna a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - Sarkin Lafia, Mai Shari’a Sidi Bage Muhammad (mai ritaya) ya yi magana kan salon mulkin Bola Tinubu.

Basaraken ya yabawa shugabancin Tinubu, inda ya ce ya sauya Najeriya kamar yadda ya yi a Legas.

Sarkin Lafia ya yabawa mulkin Tinubu
Sarkin Lafia ya kwarara yabo ga Tinubu kan ayyukan cigaba. Hoto: Bayo Onanuga, Nasarawa State Government.
Source: Facebook

Sarkin Lafia ya yabawa Bola Tinubu

Hakan na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sadarwa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna, Bafarawa ya ziyarci IBB bayan kafa sabuwar kungiyar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce Sarkin ya faɗi haka ne a fadarsa da ke Lafia a jihar Nasarawa a jiya Laraba 25 ga watan Yunin 2025.

Ya ce:

“Muna Legas lokacin da muke a kotun daukaka kara. Mun ga yadda ka juya Legas zuwa abin alfahari.
“Mai girma, kana juya wannan canjin zuwa tattalin arzikin Najeriya. Kafin ka bar ofis, Najeriya za ta zama babba."

Abin da ya burge Sarki game da Tinubu

Ya tuna yadda Tinubu ya kai ziyara lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma yadda yake daraja jagorancin shugaban tun can.

Ya kara da cewa:

“Mai girma, shugabanmu, abokinmu, komai namu. Barka da zuwa. Nan ka fara ziyararta shekaru da suka wuce.
“Na faɗa cewa kana nan sau biyu yayin yaƙin neman zaɓe. Mun yi sa’a lokacin, Buhari ya kawo ziyara kuma na yabawa Tinubu."
An yabawa Tinubu a kokarinsa na matar da Najeriya kamar Lagos
Bola Tinubu ya yabawa salon mulkin Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Tinubu ya yi magana da Sarki ya yaba masa

Sarkin wanda ke jagorantar Majalisar Sarakunan Nasarawa, ya yi alkawarin ci gaba da goyon baya ga Tinubu da gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

1447 AH: Gwamna Kirista ya ba da hutun sabuwar shekarar Musulunci a jiharsa

Shugaba Tinubu ya nuna godiya bisa tarba mai daɗi, ya ce zai ci gaba da taimaka wa jihar Nasarawa wajen albarkatu, noma da ababen more rayuwa.

“Na yi farin cikin dawowa Nasarawa. Sarki ya faɗa min a 2023 cewa zan dawo a matsayin shugaban ƙasa. Na gode.
“Kana da hangen nesa, kana da gaskiya da mutunci. Kai ɗan Najeriya ne mai jajircewa da basira."

- Cewar Bola Tinubu

Ya yaba wa Gwamna Abdullahi Sule bisa amfani da kuɗi yadda ya kamata, yana aikin manyan ayyuka ba tare da aro ba wurin samar da ayyukan alheri.

Gwamna ya fadi abin da ke damunsa a mulki

Kun ji cewa Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi tsokaci kan shekaru kusan shida da ya kwashe a ofis yana mulki.

Gwamna Sule ya bayyana cewa a cikin waɗannan shekarun ya gudanar da ayyukan da jama'a suke yabonsu saboda su.

Sai dai, ya nuna cewa duk da haka akwai ayyukan da suke sanya shi cizon yatsa saboda har ya bar mulki ba za su kammalu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.