Sabon sarkin Lafia zai shiga fada a gobe Juma'a

Sabon sarkin Lafia zai shiga fada a gobe Juma'a

- Sabon sarkin Lafia, Justis Sidi Dauda Bage, zai shiga fadar Lafia a gobe Juma’a

- Justis Sidi zai baro gidansa da ke Abuja zuwa masarautar na Lafia

- Ana sanya ran alkalin zai shiga fada, sannan kuma ya gudanar da Sallar Juma’a na farko a matsayin sarki a babbar masallacin Juma’a da ke fadar

Sabon sarkin Lafia, Justis Sidi Dauda Bage, zai shiga fadar Lafia a gobe Juma’a, 5 ga watan Afrilu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wani hadimin sabon sarkin ya bayyana cewa an kammala shiri tsaf domin komawar sarkin fada daga Abuja, inda yake alkalanci a kotun koli, sannan ya kama mulki a matsayin sarkin Lafia na 17.

Sabon sarkin Lafia zai shiga fada a gobe Juma'a

Sabon sarkin Lafia zai shiga fada a gobe Juma'a
Source: UGC

Majiyar ta kara da cewa masu rike da sarauta da dama a Lafia sun yi tattaki zuwa Abuja domin kwasar gaisuwa a wajen sabon sarkin.

Ana sanya ran alkalin zai shiga fada a matsayin sarki, sannan ya samu karramawa na musamman daga masu rike da mukamai, hakimai sannan kuma ya gudanar da Sallar Juma’a na farko a matsayin sarki a babbar masallacin Juma’a da ke fadar.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta cafke zunzurutun kudi har N54m a filin jirgin sama na Maiduguri

Idan za ku tuna an sanar da Justis Sidi Dauda Bage a matsayin sarkin Lafia na 17 a ranar 26 ga watan Maris, 2019 bayan mutuwar marigayi sarki, Alhaji Isa Mustapha Agwai, a ranar 10 ga watan Janairu, yana da shekaru 84 bayan ya shafe shekaru 44 yana sarauta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel