1447 AH: Gwamna Kirista Ya ba da Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci a Jiharsa
- Gwamna Seyi Makinde ya ayyana Juma’a, 27 ga Yunin shekarar 2025, a matsayin hutun ma'aikata a fadin jihar Oyo da ke Kudancin Najeriya
- Gwamnan ya ba da hutun ne don bikin shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1447 AH da ake sa rai a ranar Juma'a mai zuwa
- Sanarwar ta fito daga sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Olanike Adeyemo, inda aka ce hutun ya shafi ma’aikatu da cibiyoyi na gwamnati baki ɗaya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde ya zama na farko da ya fara ba da hutun sabuwar shekarar Musulunci a wannan karo.
Makinde ya ayyana Juma’a, 27 ga Yuni, 2025, a matsayin hutu domin tunawa da sabuwar shekarar Musulunci ta 1447 AH.

Source: Facebook
Sanarwar hakan ta fito ne a cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jiha, Farfesa Olanike Adeyemo, ya fitar a ranar Laraba, cewar Leadership.

Kara karanta wannan
'Har gida muka cin masa': Gwamnatin Zamfara ta faɗi illar da ta yi wa Bello Turji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Makinde ke kokarin adalci ga Musulmi
Gwamna Makinde yana kokari wurin tabbatar da cewa ya ba da hutun sabuwar shekarar Musulunci a kowace shekara da ta zagayo.
Ko a bara ma, Makinde yana kusan na farko cikin gwamnoni da suka ayyana ranar 1.ga watan Muharram a matsayin ranar hutu saboda ma'aikata su sarara.
Daga bisani, Gwamnan Oyo ya biyo bayansa duk da cewa duka gwamnonin Kiristoci ne amma an yaba musu kan kokarin yin adalci tsakanin addinai da ke jiharsu.

Source: Facebook
Musabbabin ba da hutun sabuwar shekarar Musulunci
Gwamnan ya ce an ware wannan rana ne domin bai wa Musulmi da sauran mazauna jihar damar murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci tare da nazarin mahimmancinta.
Gwamna Makinde ya kuma bukaci jama’a su yi amfani da damar wajen yin addu’o’i domin ci gaba da samun zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasar Oyo da Najeriya.
Sanarwar ta ce:
“Gwamnan ya bukaci kowa da kowa da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jiha da ƙasa baki ɗaya."
Wurare da ma'aikatu da hutun ya shafa a Oyo
Gwamnatin jihar ta ce hutun ya shafi dukkan ofisoshi da cibiyoyin gwamnati a faɗin Jihar Oyo a Kudu maso Yammacin Najeriya.
Daga bisani, gwamnan ya kuma taya al'ummar Musulmi murnar zagayowar sabuwar shekara inda ya bukaci su yi addu'o'i ga jihar Oyo da kuma siyasar da ke tunkarowa.
Gwamnonin da suka ba da hutu a bara
A baya, kun ji cewa gwamnonin jihohi a Najeriya daga Arewacin Najeriya zuwa Kudancin kasar sun ba da hutun sabuwar shekarar Muslunci ta 1446 AH.
Akalla jihohi 10 a Najeriya sun ayyana ranar Litinin 8 ga watan Yulin 2024 a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 bayan Hijrah.
A wannan shekara ma ana sa ran jihohi da dama za su ba da hutun da ake tsammanin zai fado ranar Juma'a 27 ga watan Yunin 2025 da muke ciki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
