An Yi Rashi: Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Rasu Yana da Shekara 84
- Mutuwa ta ratsa jihar Kwara bayan rasuwar tsohon gwamna wanda ya rasu yana da shekara 84 a duniya kafin ya koma ga mahaliccinsa
- Cornelius Adebayo wanda ya taɓa yin sanata ya rasu ne da safiyar ranar Laraba, 25 ga watan Yunin 2025 a birnin tarayya Abuja
- Tsohon gwamnan ya kasance ɗan gwagwarmaya a lokacin da yake raye inda yake cikin mutanen da suka riƙa sa'insa da gwamnatin soja
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kwara - Tsohon gwamnan jihar Kwara, Cornelius Olatunji Adebayo, ya riga mu gidan gaskiya.
Cornelius Olatunji Adebayo wanda yake tsohon sanata ya rasu ne a ranar Laraba, 25 ga watan Yunin 2025.

Source: Facebook
Majiyoyi daga iyalinsa sun shaida wa jaridar TheCable cewa marigayin ya rasu ne da safiyar ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin ya rasu ne yana da shekara 84 a duniya, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Kara karanta wannan
Sanata Ningi ya dauki zafi, yana son majalisa ta binciki rashin biyan yan kwangila hakkokinsu
Wanene tsohon gwamna Cornelius Adebayo?
An haifi Cornelius Olatunji Adebayo a ranar 24 ga watan Fabrairu, 1941, a garin Igbaja da ke cikin Jihar Kwara.
Marigayin ya zama gwamnan jihar Kwara a shekarar 1983, amma bai dade ba a ofis sai gwamnatin soja ta hambarar da gwamnatin farar hula.
Ya kasance ministan harkokin sadarwa daga 2003 zuwa 2006, sannan kafin nan, an zaɓe shi a matsayin sanata a shekarar 1979 a ƙarƙashin jam’iyyar UPN.
Cornelius Olatunji Adebayo ya kasance ɗaya daga cikin ƴan gwagwarmayar dimokuraɗiyya a ƙarƙashin ƙungiyar NADECO wacce ke fafutukar dawo da nasarar da aka bai wa MKO Abiola a zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga watan Yuni, 1993.

Source: Original
Tsohon gwamnan ya ki karbar kujerar minista
A shekarar 1993, gwamnatin mulkin soja ta Sani Abacha ta yi wa Cornelius Adebayo tayin muƙamin minista, amma ya ƙi amincewa da tayin.
A ranar 31 ga watan Mayu, 1995, wani bam ya fashe a birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara. Hukumar ƴan sanda ta kama Cornelius Adebayo da wasu ƴan NADECO tare da tsare su kan al’amarin.
Cornelius Olatunji Adebayo ya gudu daga Najeriya a shekarar 1996 zuwa ƙasar Canada domin neman mafaka na ɗan wani lokaci, bayan da rahotanni suka ce gwamnatin soja na neman cafke shi a karo na biyu.
Ana yabawa Cornelius Adebayo kan ɗumbin gyare-gyare a fannin ilimi a jihar Kwara lokacin da yake kwamishinan Ilimi daga 1975 zuwa 1978.
Karanta wasu labaran kan rashe-rashe
- Cashman: Shugaban 'Yan Fim Ya Rasu, Ali Nuhu da Sauran Jarumai Sun Yi Jimami
- Lokaci Ya Yi: Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Rasu Yana Kusa da Cika Shekara 90
- Lokaci Ya Yi: Tsohon Mataimakin Gwamna a Najeriya Ya Rasu
Basarake ya rasu a jihar Oyo
A wani labarin kuma, kun ji cewa Allah ya yi wa Oniroko na Irokoland da ke ƙaramar hukumar Akinyele a jihar Oyo, Mai martaba Sunmaila Olasunkanmi Abioye Opeola (Kurunloju 1) rasuwa.
Marigayin ya yi bankwana da duniya ne a ranar 30 ga watan Mayun 2025 bayan ya kwashe dogon lokaci yana kan kujerar sarauta.
Rasuwarsa ta sanya mutanen garin cikin jimami saboda kasancewarsa jagora mai kishin al'ummar da yake jagoranta.
Asali: Legit.ng
