Gwamna Fintiri Ya Cire Rawanin Atiku, an Raba Shi da Matsayin Wazirin Adamawa
- Gwamnatin Adamawa ta soke sarautar Wazirin Adamawa da ke hannun Atiku Abubakar saboda sabuwar doka da ta takaita mukaman gargajiya
- Atiku Abubakar na daga cikin wadanda wannan mataki ya shafa, duba da cewa ya fito ne daga yankin Jada, ba daga cikin masarautar Yola ba
- Masu sharhi na ganin wannan mataki yana da nasaba da takaddama mai zurfi tsakanin Umaru Fintiri da tsohon mataimakin shugaban kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa - Gwamnatin jihar Adamawa ta kawo dokar da soke sarautar Wazirin Adamawa da aka ba tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Hakan na zuwa ne saboda wani sabon tsarin da ya tanadi cewa dole sai mutum ɗan asalin masarauta ne kafin a ba shi mukamin gargajiya.

Source: Facebook
The Guardian ta wallafa cewa sanarwar ta fito ne a ranar 20 ga Yuni, 2025, ta hannun babbar sakatariyar ma’aikatar kula da harkokin sarauta, Adama Felicity Mamman.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin gyare-gyaren da gwamnatin Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri ke aiwatarwa.
Wazirin Adamawa na ɗaya daga cikin manyan mukamai masu daraja a masarautar Adamawa, kuma ana ɗaukarsa da daraja sosai.
Dalilin raba Atiku da Wazirin Adamawa
Sanarwar ta ce daga yanzu 'yan Yola ta Kudu, Yola ta Arewa, Girei, Mayo-Belwa, Song da Zumo ne kawai za su riƙe mukaman majalisar sarauta da masarautar Adamawa.
Vanguard ta wallafa cewa Atiku wanda yake daga Jada da ke cikin masarautar Ganye, ya fita daga cikin waɗanda doka ta amince su rike sarautar Waziri a yanzu.
Wannan sauyi ya shafi sauran masu sarauta da ba su fito daga yankunan da aka kayyade ba, inda za su rasa mukamansu bisa sabon tsarin da gwamnati ke kokarin aiwatarwa.
Meyasa aka cire Atiku a Wazirin Adamawa?
Gwamnatin Adamawa ta ce wannan mataki na daga cikin gyare-gyaren da ke da nasaba da sabuwar dokar kafa sababbin masarautu a jihar.
Masu nazari na siyasa na ganin lamarin ba zai rasa nasaba da rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fintiri da Atiku ba.

Source: Facebook
A shekarar 2023, Atiku da Fintiri sun kasance a jam’iyyar PDP, amma a halin yanzu ana ganin akwai rashin jituwa tsakanin su.
Hakan ya kara bayyana ne bayan yunkurin Atiku na hada kawunan wasu fitattun ‘yan siyasa irin su Nasir El-Rufai, Peter Obi da Aishatu Binani domin kafa hadakar ‘yan adawa gabanin 2027.
Sabon kudirin masarauta a Adamawa
Wani sabon kudiri da ke gaban majalisar dokokin jihar Adamawa na neman bai wa gwamna ikon tube sarakuna da kuma nada sababbin shugabanni ba tare da la’akari da tsarin gargajiya ba.
Masu sukar sa sun bayyana damuwa cewa wannan kudiri na iya bai wa gwamna karfin iko fiye da kima a harkokin gargajiya, wanda hakan zai iya haifar da tangarda da rikice-rikice.
Atiku ya gana da 'yan siyasa a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gana da wasu 'yan siyasar Arewa ta Yamma.
Atiku Abubakar ya gana da 'yan siyasar ne bayan sun nuna takaici kan goyon bayan Bola Tinubu a zaben 2023.
A yayin taron, Atiku ya zanta da wasu 'yan Kannywood domin duba yadda za su kawo sauyi da cigaba a siyasar 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


