'Yadda Isra'ila Ta Ɗauki Darasi tare da Neman Sulhu bayan Ragargaza daga Iran'

'Yadda Isra'ila Ta Ɗauki Darasi tare da Neman Sulhu bayan Ragargaza daga Iran'

  • Tsohon Ministan tarayya, Femi Fani-Kayode ya jinjinawa Iran bisa martanin da ta yi kan harin Isra'ila, yana cewa sun ci karensu ba babbaka
  • Fani-Kayode ya ce Iran ta bai wa Isra'ila darasi mai tsauri, inda ya kara da cewa wannan ne mafi munin abin da ya taba faruwa da su tsawon shekaru 77
  • Tsohon ministan ya zargi Isra'ila da Amurka da yunkurin kifar da gwamnatin Iran, ya kuma bukaci duniya ta tashi tsaye da adawa da zalunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ya tabo batun rikicin Iran da Isra'ila.

Fani-Kayode ya jinjinawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa abin da ya kira da tsayin daka da nasara kan Isra'ila.

Fani-Kayode ya yabawa jajircewar kasar Iran
Fani-Kayode ya taya Iran murna kan koyawa Iran darasi. Hoto: Femi Fani-Kayode, Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Fani-Kayode ya soki munafurcin Isra'ila da Amurka

Fani-Kayode ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafin Facebook a yau Talata 24 ga watan Yunin 2025.

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 da suka ja hankalin duniya a kwana 12 na yakin Iran da Isra'ila

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma bayan rikici mai zafi tsakanin kasashen biyu da ke gaba da juna.

A cikin sanarwar, tsohon ministan ya ce martanin Iran kan abin da ya kira hari babu dalili daga Isra'ila ne ya tilasta musu neman sulhu da goyon bayan Amurka.

Ya bayyana sakamakon a matsayin babban koma baya ga Isra'ila, yana cewa Isra'ila ba ta taba fuskantar irin wannan barna da karyewar kwarin gwiwa ba cikin shekaru 77.

A cewarsa, jajircewar Iran a fagen daga ta girgiza makiyanta, kuma ta dawo da mutuncin kasar a idon duniya.

Fani-Kayode ya jinjinawa Sojojin Iran bisa kulawa da suka yi wajen gudanar da “matakin soji cikin natsuwa”, yana cewa ba su kai hari kan fararen hula ba ko rusa biranen Isra'ila duk da karfin da suke da shi.

Ya kara da yabawa jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, saboda 'karfin hali, tawali’u da imani da ya nuna a lokacin rikicin.'

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Iran ta kai hari Isra'ila, 'ta rusa yarjejeniyar tsagaita wuta'

Tsohon minista ya soki kasashen Amurka da Isra'ila
Fani-Kayode ya taya Iran murnar ragargazar Isra'ila. Hoto: Getty Images.
Source: UGC

Fani-Kayode ya taya Ayatullah Khamenei murna

Tsohon ministan ya ce Isra'ila da Amurka sun kasa cimma burinsu, ciki har da lalata nukiliyar Iran, kifar da gwamnati da kisan shugabannin kasar.

Yayin da yake addu'ar dorewar tsagaita wutar, ya yi gargadi cewa ba za a iya amincewa da Isra'ila wajen kiyaye zaman lafiya ba.

Fani-Kayode ya soki “mamayar Isra’ila a yankunan Falasdinawa da hare-haren da take kaiwa Gaza”, yana kira ga duniya da ta tashi tsaye wurin adawa da zalunci da danniya.

“Yahudawa da Amurkawa ba su cimma burinsu ba na lalata dukkanin cibiyoyin habaka nukiliyar Iran da makamai, duk da ikirari.
“Sun kuma kasa kashe Ayatollah Khamenei, su kifar da gwamnati ko tayar da rikicin da zai rikide zuwa yaki a Gabas ta Tsakiya.
“Ina taya Jamhuriyar Musulunci ta Iran murna saboda tsayawa tsayin daka da koya wa Yahudawa da masu tayar da hankali darasi, har suka koma neman taimako a wajen Amurka."

Kara karanta wannan

'Kun shiga uku': Iran ta faɗi abin da za ta yi wa Amurka bayan hari a cibiyoyin nukiliyarta

- Cewar Fani-Kayode

Malamin Musulunci ya soki harin Iran a Qatar

Kun ji cewa shehin malamin Musulunci, Malam Aliyu Muhammad Sani ya yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai a Qatar da Iraq.

Malamin ya ce a nufinsu an yi harin ne a matsayin ramuwar gayya kan Amurka da ta farmaki Iran a karshen mako.

Sai dai malamin ya ce harin da aka kai kasashen biyu, ya sabawa ƙa’idar Musulunci da haɗin kan ƙasashen Musulmi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.