'Sarki Ya Yi Barazanar Korar Musulmi bayan Sanya Musu Haraji a Ondo,' MURIC
- Wasu masu shigar dodanni sun kai hari a masallaci da gidan limami a Oke Agbe, Jihar Ondo, inda suka doki matarsa da ’ya’yansa
- MURIC ta ce sarkin garin ya yi wa Musulman da aka zalunta tara, tare da barazanar korarsu daga gari idan ba su biya tarar awaki da tumaki ba
- Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta ce lamarin ya ci karo da tsarin mulki, tare da neman a hukunta masu laifi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - Wasu masu shigar dodanni sun kai hari a wani masallaci da gidan limami a garin Oke Agbe, shiyyar Akoko a Jihar Ondo, inda suka doki iyalan limami, matansa da ’ya’yansa.
An ce maimakon sarkin garin ya yi tir da harin, ya juya alhakin kan Musulman da aka zalunta, yana yi musu tara tare da barazanar korarsu.

Kara karanta wannan
Ana zargin Sarki da kokarin hana yin addinin Musulunci bayan hari kan limami, masallaci

Source: Twitter
Aminiya ta rahoto cewa kungiyar MURIC ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce wannan abu ne da bai dace ba a karkashin dimokuraɗiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar MURIC ta ce sarki ya ci tarar Musulmi
A cewar MURIC, bayan da mutanen suka kai harin ranar Alhamis 12 ga Yuni, sarkin Oke Agbe bai dauki wani mataki na kare Musulman da aka ci zarafinsu ba, sai ma ya tuhume su.
Sanarwar da shugaban MURIC ya fitar ta ce:
“Ya bukaci su biya tarar awaki tara, tumaki bakwai ko kuma a haramta musu zama a garin,”
Kungiyar ta bayyana cewa hakan ya nuna tsantsar wariya da nuna kyamar Musulmi a yankin, wanda ke kara dagula zaman lafiyar al’umma a Kudu maso Yamma.
MURIC ta nemi a dauki matakin shari’a
Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana harin da kuma martanin sarkin a matsayin wani lamari da ya wuce gona da iri.

Kara karanta wannan
Sarki ya shiga uku, bayan dakatar da shi, an tura shi gidan yari kan kalaman ɓatanci
Ya bayyana haka yana mai cewa abin da ya faru wata alama ce da ke kara tayar da hankali a kan halin da Musulmi ke ciki a yankin.
Ya ce:
“Abin takaici ne a ce a ƙarni na 21 da tsarin mulkin ƙasa ke tabbatar da ’yancin addini, a ce akwai basarake da ke barazanar korar Musulmi daga garinsu saboda sun kare kansu daga hari,”
Ya ce ba za su yarda da irin wannan cin zarafi ba, yana mai cewa dole ne gwamnatin Jihar Ondo ta dauki mataki don tabbatar da adalci.
MURIC ta bukaci gwamnati ta sa baki
Kungiyar MURIC ta bukaci gwamnatin jihar Ondo da ta duba wannan lamari da idon adalci, tare da hukunta duk wanda ke da hannu a harin ko kuma cin zarafin Musulmin.
MURIC ta ce dole ne a tabbatar da cewa ba a yi wa limamin ko iyalansa wani mummunan abu ba, kuma a janye maganar haramta musu zama a garin.

Source: Twitter
Yawan Musulmai ya karu a duniya
A wani rahoton, kun ji cewa wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa adadin Musulmai na kara yawa a duniya.
Rahoton ya tabbatar da cewa Musulunci ya zama addini daya tilo da yawansa ke karuwa ba tare da raguwar mabiya ba.
Legit ta rahoto cewa yawan da Musulmai ke karawa na cike gibin tazarar da ke tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kiristanci a duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
