Ana Zargin Sarki da Kokarin Hana Addinin Musulunci bayan Hari kan Limami, Masallaci
- Wasu masu shigar dodanni sun kai hari kan gidan babban limamin wani gari a Ondo da kuma masallacinsa, inda suka lakada wa iyalansa duka
- Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta soki harin, ta kira shi da barna, rashin hankali kuma abin ta da hankali tare da neman a hukunta masu laifin
- Farfesa Ishaq Akintola ya ce Sarkin maimakon ya hukunta masu laifi, sai ya ci tarar limamin da iyalinsa, tare da barazanar kora
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - Kungiya mai kare hakkin Musulmi, watau 'Muslim Rights Concern' (MURIC) ta yi Allah wadai da kai hari kan limami.
Kungiyar MURIC ta bukaci rundunar ’yan sandan Jihar Ondo ta kama tare da gurfanar da masu shigar dodanni da suka kai hari.

Source: Original
An farmaki limami da iyalansa a Ondo
An bayyana cewa wasu masu shigar dodanni (Masquerades) sun shiga masallaci da gidan babban limamin garin, inda suka yi wa matansa da ’ya’yansa duka, cewar Vanguard.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a gano dalilin wannan hari ba wanda ya jawo cece-kuce da zargin tauye hakkin yin addini.
Yayin da take mayar da martani, MURIC ta yi Allah wadai da harin kan limamin da kuma masallacinsa.
Kungiyar ta yi zargin cewa Sarkin ya ci tarar iyalan da kuma kokarin hana addinin Musulunci a garin baki daya.

Source: Twitter
MURIC ta fusata saboda hari kan limami
Ƙungiyar ta bayyana harin da cewa barna ne, rashin hankali da kuma abin ta da hankali ne, cewar rahoton PM News.
Daraktan kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa.
Ya ce:
"Bayan harin, Sarkin garin ya ci tarar wadanda aka ci zarafi maimakon hukunta wadanda suka aikata laifin.”
“An umurci Limamin da iyalinsa da su kawo awaki tara, tumaki bakwai da goro saboda matan sun yi ihu da zagi lokacin da ake dukansu.”
“An bayyana cewa idan har ba su kawo kayan da aka bukata ba kafin Litinin, za a kori dangin daga garin, kuma a hana Musulunci gaba ɗaya.”
Yadda hankulan al'umma ya tashi a Ondo
Wannan lamari ya tayar da hankula a yankin wanda ya jawo zaman dar-dar da tsoron abin da ka iya biyo baya kan harin da aka kai da ke nufin kokarin hana addinin Musulunci.
Babban abin da ya ta da hankali shi ne rashin sanin takamaiman dalilin farmakin da kuma gazawar hukumomi wurim daukar matakin da ya dace.
MURIC ta zargi Tinubu da fifita Kiristoci
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar kare haƙƙin Musulmi, MURIC, ta zargi gwamnatin tarayya da nuna bambanci a harkar jigilar fasinjoji kyauta yayin bukukuwan addini.
MURIC ta ce gwamnatin ta ware Kiristoci da ba su damar hawa jirgin kasa kyauta a lokacin Kirsimeti, amma ba ta yi hakan ga Musulmi a lokacin sallah ba.
Ta yi kira da a duba tsarin hutun karshen mako da bukukuwan kasa da ta ce sun fi karkata ga Kiristanci tun daga zamanin mulkin mallaka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

