Emefiele: Kotu Ta Jiƙa Aiki, Ta Sauya Hukuncin Kwace Kadarorin Tsohon Gwamnan CBN
- Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin kwace kadarori da makudan kudi daga hannun tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- Alkalin kotun ya ce akwai ruɗani a hujjojin da lauyoyin Emefiele da EFCC suka gabatar, ya umarci babbar kotun tarayya ta sako shari'ar daga farko
- Tun farko ƙaramar kotun ta kwace kadarorin da ake zargin suna da alaƙa da Emefiele bisa hujjojin da hukumar EFCC ta gabatar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Kotun ɗaukaka kara mai zama a jihar Legas ta soke hukuncin ƙwace wasu kadarorin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
A hukuncin da ta yanke mafi rinjaye, wanda alkalai biyu cikin uku suka goyi baya, kotun ta umarci a sake duba shari'ar tun daga farko saboda akwai ruɗani.

Source: Facebook
Hukuncin, wanda aka yanke tun ranar 9 ga watan Afrilu, 2025, ya shiga hannun wakilin jaridar Tribune Nigeria ranar Lahadi, 15 ga watan Yuni, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane hukunci aka soke kan kadarorin Emefiele
A baya dai, babbar kotun tarayya da ke Legas ta bayar da umarnin kwace kadarori da kudi na Emefiele a ranar 1 ga Nuwamba, 2024, bayan amincewa da buƙatar EFCC.
Kadarorin da aka ƙwace daga hannun Mista Emefiefe sun haɗa da gidaje da filaye na biliyoyin Naira, daga ciki akwai wasu a No. 17B, Hakeem Odumosu Street, Lekki Phase 1, Legas.
Baya ga haka, kotun ta kuma bayar da umarnin kwace $2,045,000 da takardun hannun jari a kamfanin Queensdorf Global Fund Limited, duk ta mika su ga Gwamnatin Tarayya.
Hukumar EFCC ta yi zargin cewa Emefiele ya mallaki wadannan kadarorin ne daga kudaden haram, waɗanda ya samu ta hanyoyin da suka saɓa doka.
Sai dai Emefiele bai gamsu da hukuncin ba, inda ya daukaka kara ta hannun lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Olalekan Ojo (SAN).
EFCC ce kadai aka bayyana a matsayin wanda ake kara a karar mai lamba CA/LAG/CV/1051/24 da lauyoyin Emefiele suka shigar gaban kotun ɗaukaka ƙara.

Kara karanta wannan
Benue: yan bindiga sun banka wa gidaje da ƴan gudun hijira wuta, mutane fiye da 200 sun mutu

Source: Facebook
Kotun ɗaukaka kara ta yanke hukunci
Amma a hukuncin da Mai Shari’a Abdulazeez Anka ya yanke, ya ce akwai yiwuwar albashin halal na Emefiele na iya ba shi damar sayen wadannan kadarorin.
Mai shari'a Anka ya ce:
"Kudaden da aka nuna na halal ne, kamar yadda ya bayyana. Kuma da albashinsa tun daga lokacin da yake a Zenith Bank har zuwa matsayin Gwamnan CBN na tsawon shekaru 10, yana iya mallakar wadannan kadarori.
“Don haka, kotu ta soke umarnin kwace kadarorin da kotun farko ta bayar a ranar 1 ga Nuwamba, 2024."
Sai dai alƙalin ya ce akwai ruɗani a hujjojin da ɓangarorin biyu suka gabatar, don haka ya ba da umarnin sake sauraron shari'ar a babbar kotun tarayya.
Kotu ta yi watsi da buƙatar Emefiele
A wani labarin, kun ji cewa wata kotu a jihar Legas ta yi fatali da buƙatar tsohon gwamnan babban banki watau CBN, Godwin Emefiele.
Emefiele ta bakin lauyansa, Olalekan Ojo (SAN), ya kalubalanci iko da hurumin kotun wajen sauraron kara da Hukumar EFCC ta shigar a kansa.
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Rahman Oshodi, ya bayyana cewa kotun na da ikon sauraron shari’ar Emefiele da kuma wanda ake tuhuma tare da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

