Duk da Karrama Shi da Lambar Yabo, Soyinka Ya Cire Kunya, Ya Ƙalubalanci Tinubu
- Farfesa Wole Soyinka ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya binciki mutuwar Dele Giwa, Kudirat Abiola da Bola Ige domin samar da adalci
- Soyinka ya bayyana hakan ne yayin bikin ranar dimokuradiyya, inda ya ce akwai mutane da za su iya ba da shaidar abin da ya faru
- Har ila yau, ya yabawa karramawar da aka yi wa jaruman yaki da mulkin soja, amma ya ce akwai wasu muhimman sunaye da aka bari
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Duk da karrama shi da lambar yabo, Farfesa Wole Soyinka ya ba Bola Tinubu shawara kan wasu matsaloli.
Soyinka ya bukaci Bola Tinubu da ya binciki mutuwar wasu fitattun 'yan Najeriya ciki har da wadanda ya ba lambar yabo ta musamman.

Source: UGC
Kisan Kidirat, Ige: Soyinka ya shawarci Tinubu
Soyinka ya bayyana haka ne ga wasu manema labarai da aka zabo a Legas ranar Asabar, cewar Channels TV.
Ya ce dole ne a binciki yadda aka kashe Dele Giwa, Bola Ige da Kudirat Abiola don a samu gaskiya da zaman lafiya.
A yayin bikin ranar dimukraɗiyya, Shugaba Tinubu ya yi jawabi a gaban majalisar dokoki tare da ba wa wasu gwarazan yaki da mulkin soja lambar yabo.
Soyinka ya yaba da wannan karramawa, amma ya ce akwai sunayen wasu jarumai da aka manta da su a cikin jerin wadanda aka karrama.
Ya bayyana cewa zai sadaukar da lambarsa ga marigayi Beko Ransom-Kuti wanda ya ce ya kasance gwarzon kare hakkin bil’adama da ya sha tsarewa.
June 12: Gargadin Soyinka ga Tinubu
Soyinka ya gargadi gwamnati da ka da ta raina muhimmancin gwagwarmayar 12 ga watan Yuni, inda ya ce mutane da dama sun mutu ko sun jikkata.
An bayyana jerin wadanda aka karrama ranar Alhamis 13 ga Yuni, a wani bangare na bukukuwan ranar dimokuradiyya ta bana.
Daga cikin wadanda aka karrama bayan rasuwarsu akwai Shehu Musa Yar’Adua, Farfesa Humphrey Nwosu, da Kudirat Abiola matar MKO Abiola.

Source: Facebook
Yadda Tinubu ya karrama yan Ogoni
Saro-Wiwa ya samu lambar Commander of the Order of the Niger (CON), sauran takwas kuma sun samu Officer of the Order of the Niger (OON).
Wannan shi ne karon farko da Shugaban Najeriya ya amince da rawar da ’yan Ogoni tara suka taka a tarihinta na dimokuradiyya.
’Yan Ogoni tara sun fito daga kungiyar MOSOP, wacce ta yi gwagwarmaya da gurbata muhalli da kamfanonin mai suka haddasa a yankin Neja Delta.
Kisan su a 1995 ya jawo suka daga kasashen duniya, har ma da dakatar da Najeriya daga kungiyar 'Commonwealth' na wani lokaci.
Tinubu ya karrama fitattun yan Najeriya
Kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya ba marigayiya Kudirat Abiola, Janar Shehu Musa Yar’Adua da Farfesa Humphrey Nwosu lambar yabo.
Wole Soyinka da Janar Akinrinade sun samu lambar yabon GCON, yayin da Bola Ige, Balarabe Musa da sauransu suka samu CFR.
Tinubu ya karrama mutanen saboda rawar da suka taka a ci gaban dimukraɗiyya inda ya ce za a saki cikakken jerin waɗanda aka karrama nan gaba.
Asali: Legit.ng

