Ana Shirin Zaben Anambra, Gwamna Ya Kakabawa APC da Jam'iyyu 15 Harajin N800m
- Jam'iyyun siyasa 16 a Anambra za su biya N800m don samun izinin gudanar da yakin neman zabe da kafe allunan tallata 'yan takara
- Kowace jam'iyya zata biya N50m kafin fara yakin neman zabe, umarnin da ya haifar da cece-kuce daga jam'iyyu, irinsu LP da APC
- APC ta zargi gwamnatin Anambra da yunkurin rufe muryoyin 'yan adawa yayin da ta ce hakan kuma ba zai hana APGA faduwa zabe ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - An bukaci jam'iyyun siyasa 16 da za su fafata a zaɓen gwamnan Anambra a ranar 8 ga Nuwamba, su biya jimillar kuɗi N800m ga gwamnatin jihar.
An rahoto cewa biyan wannan kuɗin ne zai ba jam'iyyun siyasar damar samun lasisin kafe fastoci da allunan tallan 'yan takararsu a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Kara karanta wannan
"Ina sha'awar shiga APC saboda mutum 2," Tsohon hadimin Atiku ya yi barazanar barin PDP

Source: Facebook
Gwamnati ta kakabawa jam'iyyu harajin N50m
Kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito, gwamnatin Anambra ta bukaci kowace jam'iyyar siyasa ta biya N50m kafin a ba ta izinin kafe allunan yaƙin neman zaɓenta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito a baya cewa hukumar tallace-tallace ta jihar Anambra (ANSAA) ta buƙaci kowane ɗan takarar gwamna ya biya kuɗin izinin yakin neman zaɓe na N50m.
Tuni wannan sabon umarnin na gwamnatin Anambra ya haifar da cece-kuce a jihar, yayin da jam'iyyar LP da APC suka yi watsi da umarnin.
A cewar ɗan takarar jam'iyyar LP, Cif George Moghalu:
"Wannan wasa ne kawai, ai za mu ga wanda zai kama mutanen da ke sanye da riguna ko hulunan yakin neman zabe ko kuma a kama masu tuƙa motar yakin neman zaben."
APC ta caccaki gwamnatin jihar Anambra
Da yake mayar da martani, jagoran kungiyar dattawan APC, Cif Bunty Onuigbo, ya bayyana umarnin a matsayin wata hanya ta rufe muryoyin jam'iyyun adawa.

Kara karanta wannan
"Abubuwa sun lalace," Peter Obi ya faɗi hanya 1 da ƴan Najeriya za su ƙifar da Tinubu a 2027
"Wannan shi ne abin da suke ƙoƙarin yi don kada sauran jam'iyyun su iya yin yakin neman zabe, wanda hakan zai sa APGA ce kawai za ta yi yakin neman zaben.
"Ta yaya za mu tabbatar da cewa Gwamna Charles Soludo da APGA za su biya kudin? Ta yaya hukumar za ta kasance mai gaskiya don nuna mana shaidar biyan kuɗi daga APGA wacce ita ce jam'iyyar da ke kan mulki a halin yanzu
"Ba za su iya hana muryar jama'a ba, kuma dabarunsu ba za su iya ceto APGA daga shan kaye a zaɓen ba."
- Cif Bunty Onuigbo.

Source: Twitter
Gwamnati ta hana gina allunan tallar 'yan takara
Shugaban hukumar ANSAA, Tony Odili Ujubuonu ya shaida cewa:
"Kowace jam'iyyar siyasa za ta biya kudin izinin kafe allunan yakin zabe da ma kudin yakin neman zaben na N50m zuwa ga asusun gwamnatin jihar Anambra."
Haka nan, hukumar ta nace cewa dole ne sai an tantance dukkanin kayayyakin yakin neman zabe da aka da niyyar amfani da su a wajen hukumar kula da tallace-tallace ta Najeriya (ARCON).
Hukumar ta kuma yi gargadin cewa:
"Ba a yarda wani mutum, jam'iyyar siyasa ko ƙungiyar tallafi su gina allunan talla ko wani tsarin talla a kowane ɓangare na jihar Anambra."
Dalilai 5 da za su iya hana Soludo cin zaben Anambra
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an fara gangar siyasa a jihar Anambra yayin da wa'adin farko na Chukwuma Charles Soludo ke dab da karewa.
A shekarar 2025, al'ummar Anambra za su sake komawa rumfunan zaɓe don sake zaɓen Gwamna Soludo ko kuma wani sabon gwamna da zai mulke su.
Kafin wannan zaɓen mai zuwa na 2025, matsalolin siyasa sun fara fitowa fili. Legit.ng Hausa ta binciko dalilai biyar da ka iya zama cikas ga Gwamna Soludo a neman tazarcensa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
