Goron Sallah: Tsohon Shugaba Buhari Ya Rabawa 'Yan NYSC Kyautar Saniya

Goron Sallah: Tsohon Shugaba Buhari Ya Rabawa 'Yan NYSC Kyautar Saniya

  • Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nuna kyautatawa ga ’yan hidimar ƙasa (NYSC) da ke hidima a garinsa na Daura, jihar Katsina
  • Hukumar ta tabbatar da cewa ta karbi bada saniya da wasu kayan abinci domin su yi amfani da su wajen gudanar da shagalin bikin Sallah babba
  • An isar da kyautar ta hannun Danmadanin Daura, Musa Haro, wanda ya wakilci Buhari wajen mika kayan ga shugaban NYSC na jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bai wa ’yan hidimar ƙasa (NYSC) da ke yin hidima a ƙaramar hukumar Daura ta jihar Katsina kyautar shanu da kayan abinci.

Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na NYSC, Mista Alex Obemeata, ya fita.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jagoranci Bill Gates da Otedola zuwa matatar Dangote

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Tsohon Shugaba Buhari ya gwangwaje yan NYSC a Katsina Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Mista Obemeata ya tabbatar da cewa wannan na daga cikin kyautar da aka yi masu domin murnar bikin Sallah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya yi kyauta ga yan NYSC

A cewar sanarwar, Danmadanin Daura, Alhaji Musa Haro, ne ya mika kyautar yayin da Shugaban NYSC na jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Sa’idu, ya karɓa a madadin hukumar.

Alhaji Sa’idu, wanda Alhaji Nurudeen Salisu, jami’in kula da NYSC a ƙaramar hukumar Daura, ya wakilta, ya bayyana cewa wannan kyauta na nuna irin kyakkyawar alakar Buhari da al'umma.

Yan NYSC sun ji dadin kyautar Buhar
An bayyana cewa dama Buhari ya saba kyautar ga 'yan NYSC Hoto: National Youth Service Corps
Source: Facebook

A cewar Alhaji Nurudeen Salisu, bai wa ’yan hidima kyauta yayin bukukuwan Sallah babi ne daga cikin dabi’un tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari duk lokacin da ya dawo gida domin shagulgulan addini.

Ya ce Buhari ya jima yana bayar da kyautar tun yana kan mulki, kuma har yanzu yana cigaba da nuna kulawa ga shirin NYSC da matasan ƙasa, duk da cewa ya sauka daga mulki.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa da Tinubu ya fadawa 'yan Najeriya a sakon barka da sallah

NYSC ta yi addu’ar fatan alheri ga Buhari

Kwamishinan NYSC na jihar Katsina, Ibrahim Sa’idu, ya yi addu’ar cigaba da samun nasara ga tsohon shugaban kasar duba da kulawar da yake ba su.

Ya roka wa tsohon shugaba Buhari lafiya, tsawon rai da albarka daga Allah Subhanah wa ta'ala, tare da cicciba iyalansa.

Ibrahim Sa’idu, ya ce irin wannan girmamawa da taimako ga ’yan hidima na ƙarfafa zumunci da ƙara jin daɗin hidimar ƙasa ga matasa da ke zuwa daga sassa daban-daban na Najeriya.

An kamanta gwamnatin Tinubu da Buhari

A baya, kun ji cewa tsohon gwamna, Ayodele Fayose, ya ce halin da Najeriya ke ciki a yanzu karkashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fi sauki a kan lokacin Muhammadu Buhari.

A cewarsa, lokacin gwamnatin Buhari tattalin arziki ya durƙushe, amma yanzu ana kokarin farfaɗo da shi ta hanyoyin sauye-sauye da shirin da shugaban kasa ya zo da shi ga jama'a.

Duk da kasancewarsa jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Fayose ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Tinubu, yana mai cewa tun yana gwamna ne ya yarda da kwarewar Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng