Gwamnati Ta Kammala Shirin Ranar Dimokuradiyya, Tinubu zai Yiwa Kasa Jawabi

Gwamnati Ta Kammala Shirin Ranar Dimokuradiyya, Tinubu zai Yiwa Kasa Jawabi

  • Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka dace wajen bikin ranar dimokuradiyya ta ranar Alhamis
  • Ta ce za a fara bikin ranar da jawabin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, yayin da zai shaidawa yan kasa halin da dimokuradiyya ke ciki
  • Daga bisani zai halarci zaman majalisar dokokin kasar nan, sai dai an bayyana soke faretin da aka saba gudanarwa a bikin duk shekara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Gwamnatin Tarayya ta saki jerin abubuwan da za a gudanar a yayin bikin ranar dimokuraɗiyya ta 2025, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis, 12 ga Yuni, 2025.

A cewar wata sanarwa da Kwamitin harkokin ma’aikatu ya fitar, bikin bana zai fara ne da jawabin kasa daga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da 7.00 na safe.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Dattawan Arewa sun dira a kan masu tallata Tinubu tun yanzu

Shugaban kasa, Bola Tinubu
Gwamnati ta ce an gama shiri kan bikin rana dimokuradiyya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar The Nation ya bayyana cewa jawabin shugaban kasa zai mayar da hankali ne kan irin cigaban da Najeriya ta samu a tafiyar dimokuraɗiyyarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a kuma tabo batun sauye-sauyen da ake aiwatarwa a karkashin manufarsa, da kuma jajircewar gwamnati wajen ciyar da ƙasa gaba da adalci da dimokuraɗiyya.

Bola Tinubu zai halarci zaman majalisa

Sanarwar da Abdulhakeem Adeoye ya sa hannu a madadin Daraktan labarai da hulɗa da jama’a, ta ce da 12.00 na rana, Shugaba Tinubu zai halarci zaman hadin gwiwa na majalisar dokoki.

An bayyana cewa ba za a yi faretin bikin al’ada kamar yadda aka saba ba a bana, amma za a yi wasu muhimman taruka guda biyu da shugaban kasa zai halarta.

Wannan zama na musamman zai kasance a matsayin wata alamar haɗin kai tsakanin bangaren zartarwa da na dokoki wajen ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Za a yi lakca kan ranar dimokuradiyya

Kara karanta wannan

'Jam'iyya 1 ba za ta iya ba,' Tsohon dan takara ya fadi yadda za a kwace mulki daga Tinubu

Haka kuma, za a gudanar da wata lakca ta musamman kan dimokuraɗiyya da 4.00 na yamma a dandalin taro na fadar shugaban kasa.

An bayyana cewa wakilan kafafen yada labarai na fadar Shugaban kasa ne za su kula da yada shirye-shiryen wannan taro, tare da bukatar hadin kansu da tanadin ingantattun kayan aiki.

Shugaban kasa zai je majalisa
Tinubu zai yiwa yan kasa bayani kan ranar dimokuradiyya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ranar Dimokuraɗiyya ta bana ita ce ta biyu da aka gudanar karkashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ta zo a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan gyare-gyaren tsarin dimokuraɗiyya, sauya kundin tsarin mulki, da kuma kokarin ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Gwamnati ta sauya ranar dimokuradiyya

A baya, mun wallafa cewa a ranar 6 ga watan Yuni, 2018, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sauya Ranar dimokuraɗiyya zuwa 12 ga watan Yuni maimakon 29 ga watan Mayu.

Sanarwar ta zo kwanaki takwas bayan gudanar da bikin Ranar dimokuraɗiyya ta shekarar 2018 a ranar 29 ga Mayu, wanda aka rika amfani da ita na tsawon kusan shekara 20.

A cewar Buhari, ranar 12 ga Yuni tana da muhimmanci a tarihin Najeriya, domin a wannan rana ce aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa mafi sahihanci a tarihin ƙasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng