Takarar Gwamna: Sarki Ya Yaba wa Sheikh Pantami a Gombe, Ya Fadi Alherinsa
- Masarautar Pantami ta karrama Sheikh Isah Ali Pantami bisa irin gudunmawar da yake bayarwa ga jama’ar Gombe da Najeriya baki ɗaya
- Takardar yabon da mai martaba Hakimin Pantami ya fitar ta yaba da ayyukansa a bangaren lafiya, ilimi, tsaro da kuma kyautata rayuwa
- ‘Yan Najeriya da dama a kafafen sada zumunta sun taya shi murna, tare da yi wa malamin fatan alheri a kan ayyukan da ya saka a gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - A ranar 1 ga Yuni, 2025, masarautar Pantami a jihar Gombe ta fitar da takardar yabo ga Wazirin Pantami, Sheikh Isah Ali Ibrahim Pantami.
Rahoto ya nuna cewa an karrama tsohon ministan ne bisa irin gudunmawar da yake bayarwa ga al’ummar yankin da ma jihar Gombe gaba ɗaya.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayani da masarautar Pantami ta fitar ne a cikin wani sako da Sheikh Isa Ali ya wallafa a X.
Masarautar Pantami ta yabi Sheikh Isa Ali
Takardar ta fito ne daga ofishin Hakimin Pantami, Alhaji Yakubu Abdullahi, da 'yan fadarsa, inda suka yaba da yadda Sheikh Pantami ke aiwatar da ayyukan ci gaba a fannoni da dama.
An bayyana cewa irin jagorancin Pantami a bangaren lafiya, ilimi, tsaro da taimakon jama’a ya zame wa al’umma ginshiƙi mai ƙarfi da abin alfahari.
Hakimin Pantami ya kammala takardar yabo da fatan alherin da cewa:
"Muna fatan Allah ya ƙara maka arziki da lafiya.”
Jama’a sun taya Sheikh Pantami murna
Bayan fitar da takardar yabo daga Hakimin Pantami, jama’a da dama sun cika kafafen sada zumunta da sakonnin taya murna da addu’o’i ga Sheikh Pantami.
Engr Al Ameen Musa ya rubuta:
“Ko da yake muna da bambanci na akida – ni mabiyi Tijjaniya ne – ina girmamaka, kuma da izinin Allah zan cigaba da maka addu’a. Allah ya kai ka ga zama Gwamnan Gombe, Amin.”

Kara karanta wannan
'Dan jihar Jigawa ya zama dan Afrika na farko da ya lashe kyautar fassara a Saudiyya
Shi ma Gaisa Gumel ya bayyana farin cikinsa da cewa:
“Masha Allah, muna taya ka murna bisa wannan yabo da ya dace da kai.”
Matasan Gombe sun roki kulawar Pantami
A karkashin rubutun malamin, Dàñ Abdàllàh, a madadin Alkahira Youth Development Forum, ya rubuta cewa:
“Dukkan godiya ta tabbata ga Allah. Muna isar da sakonmu ga Farfesa Pantami da ya dubi halin da muke ciki da idon rahama.
Muna da ƙwazo, amma rashin damar shiga shirye-shiryensa ya hana mu cin gajiyar tallafinsa.”
Wannan kiran na nuni da yadda matasa ke kaunar samun damar amfana da shawarwari ko guraben ci gaba daga fitattun shugabanni kamar Sheikh Pantami.

Source: Facebook
Wani ɗan siyasa da ke amsa sunan Hamza Dadum Hon ya ce:
“Muna taya ka murna bisa wannan karramawa da ka samu wanda ka cancanta da ita. Allah ya ba ka ikon rike girman da aka ba ka.”
Akwai yiwuwar Pantami ya yi takara a 2027
A halin yanzu, akwai ƙaruwa da yawa na hasashe da jita-jita a tsakanin al’ummar jihar Gombe da kafafen sada zumunta cewa Sheikh Isah Ali Pantami na iya tsayawa takarar gwamna a zaben 2027.
Wannan zato ya samo asali ne daga irin karbuwa da shahara da ya ke da ita a cikin al’umma, da kuma ayyukan alheri da ya ke gudanarwa a fannoni da dama tun bayan barinsa kujerar Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani.
Masu sharhi da jama’a sun nuna cewa irin tasirin Sheikh Pantami a bangaren ilimi da kyautata rayuwar al’umma ya sanya ya samu tagomashi daga matasa da dattawa.
Hakanan, yadda masarautu ke karrama shi da yabo kan ayyukansa ya kara tunzura hasashen cewa zai iya juyawa zuwa siyasa.
A shafukan sada zumunta, wasu na masa addu’a da fatan Allah ya kai shi kujerar mulki domin ya kara baje irin gudunmawar da ya saba.
Ko da yake Sheikh Pantami bai fito fili ya bayyana niyyarsa ba, ganin yadda yake jan hankalin jama’a da ayyukan raya kasa na iya zama ginshiki ga kowane yunkurin siyasa da zai iya shiryawa a gaba.
Legit ta tattauna da Naziru Usman
Wani matashi a jihar Gombe, Naziru Usman ya ce masarautar Pantami ta yi daidai da ta karrama Sheikh Isa Ali Pantami.
Matashin ya ce:
"Duk da cewa har yanzu Malam bai fito karara ya bayyana cewa zai yi takara ba, amma lokaci muke jira kawai.
"Ya taba cewa komai da lokacinsa, saboda haka muma lokacin muke jira."
Labarin haduwar Pantami da 'yan fashi
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya ba da labarin yadda ya kubuta daga sharrin 'yan fashi a shekarun baya.
Malamin musuluncin ya bayyana cewa ya taba haduwa da 'yan fashi a hanyar zuwa Maiduguri daga jihar Gombe.
Ya ce wani dan fashi ya yi kokarin harbinsa da bindiga amma saboda yadda ya rika yin addu'a mugun bai samu nasara a kan shi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


