Gwamna Zulum Ya Ba da Tallafi ga Mutanen da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Neja
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya je ziyarar jaje domin ambaliyar ruwan da ta auku a jihar Neja
- Babagana Umara Zulum bayan yi wa gwamnati ta'aziyya ya kuma ba da gudunmwar N300m domin tallafawa mutanen da ambaliyar ta shafa
- Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya yaba bisa gudunmawar da Zulum ya ba da, inda ya sha alwashin cewa za a yi amfani da su yadda ya dace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bayar da tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Mokwa.
Gwamna Zulum ya ba da gudunmawar N300m ga waɗanda ambaliya ta shafa a ƙaramar hukumar Mokwa da ke jihar Neja.

Source: Facebook
Zulum ya sanar da bayar da tallafin ne a ranar Talata, lokacin da ya jagoranci wata tawaga daga jihar Borno zuwa gidan gwamnati da ke Minna, cewar rahotom tashar Channels tv.

Kara karanta wannan
Al'umma sun shiga mummunan firgici bayan ƙaramar girgizar ƙasa ta faru a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Zulum ya je jihar Neja
Gwamna Zulum ya je ne domin yin ta'aziyya ga gwamnatin Neja da mutanenta bisa ibtila'in ambaliya da ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 200 tare da raba dubban mutane da muhallansu, rahoton The Punch ya tabbatar.
Ya ce an bayar da gudummawar ne domin tallafawa kan ƙoƙarin da gwamnatin jihar Neja ke yi wajen ɗaukar mataki kan ibtila’in wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayuka, rushe gidaje, lalata gonaki da asarar hanyoyin samun abin rayuwa.
"Lokaci ya yi da gwamnatocin jihohi za su haɗa kai domin rage illar sauyin yanayi wanda ke haddasa irin waɗannan bala'o'i."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Haka zalika, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da tsari mai ɗorewa domin fuskantar matsalolin ambaliya da sauran ƙalubalen da suka shafi sauyin yanayi.
Gwamna Bago ya yabawa Zulum
A nasa jawabin, gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya bayyana matuƙar godiya bisa wannan ziyarar da kuma kyautar kuɗin, yana mai cewa an ba da su a kan lokaci kuma ya nuna cikakken haɗin kai da ƴan'uwantaka

Source: Facebook
Gwamna Bago ya jaddada tarihin dangantaka mai kyau da ke tsakanin jihohin Borno da Neja, yana yaba wa jajircewa, tausayi da hangen nesa da Gwamna Zulum ke nunawa, wanda ya ce yana ci gaba da zama abin koyi ga sauran shugabanni.
Ya tabbatar wa da ɗan uwansa Gwamna Zulum cewa za a yi amfani da kuɗaɗen da aka bayar yadda ya kamata, wajen tallafawa al’ummomin da abin ya shafa da kuma ci gaba da ƙoƙarin sake daidaita rayuwar su da wayar da kan jama'a.
Haka kuma, ya jaddada muhimmancin faɗakar da jama’a game da haɗarin zama a kusa da koguna ko wuraren da ke da haɗarin ambaliya domin kaucewa afkuwar irin wannan bala’i a nan gaba.
Gwamna Bago ya ba da tallafin N1bn
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ba da tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a garin Mokwa.

Kara karanta wannan
Gwamna Zulum ya tuna da iyalan sojojin da suka rasu a fagen daga, ya ba su tallafi
Gwamna Bago ya ba da tallafin N1bn domin rage raɗaɗi ga mutanen da ambaliyar ruwan ta ritsa da su a Mokwa.
Umaru Bago ya kuma ba da kwangilar ayyukan da za su lashe N7bn domin samar da ababen more rayuwa yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
