Yan Bindiga Sun Farmaki Kwamishina da Wasu Mutum 3, an Fadi Halin da Suke Ciki
- Yan bindiga sun kai hari kan wani kwamishina yayin wani farmaki da suka kai kan wasu al'umma a Imo da ke Kudancin Najeriya
- Kwamishinan mai suna Chaka Chukwumerije, da wasu Bayin Allah uku sun tsira daga harin da miyagun suka kai a jihar
- Rundunar ‘yan sanda ta Abia ta ce lamarin ya faru a yankin Imo, yayin da dan uwansa, Dike ya tabbatar da harin a inda ya yi Allah wadai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Owerri, Imo - Kwamishinan filaye na Abia, Chaka Chukwumerije da wasu mutane uku sun tsallake rijiya da baya bayan harin yan bindiga.
Kwamishinan da sauran mutanen sun tsira daga harin yan bindiga da ake zargin sun kai a daren Asabar 7 ga watan Yunin 2025 a jihar Imo.

Source: Original
Yan bindiga sun farmaki kwamishina a Imo
Jaridar Punch ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a Ezinnachi, kan hanyar Enugu-Umuahia a jihar Imo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ya yi godiya ga Ubangiji da ya tseratar da shi daga harin yan bindiga a yankin.
Ya bayyana cewa:
“Godiya ta tabbata ga Allah, na tsira daga hari a kan hanyata daga Umunneochi zuwa Umuahia, sun yi wa motarmu ruwan harsashi, ya kusa zuwa inda nake zaune.”
“Da muka wuce kwanar Okigwe, muna kusa da Ezinnachi a jihar Imo, sai muka ga wata mota tana zuwa tamkar tana zuwa gefen hanya daya.
“Muka taka birki domin fahimtar abin da ke faruwa. Kafin mu ankara, daga inda nake zaune ne suka bude wuta.
"Muna godewa Allah da muka tsira, mun dawo Umuahia lafiya.”

Source: Twitter
Abin da yan sanda suka ce kan harin
Rahotanni sun nuna cewa kwamishinan yana tare da wasu mutane uku a lokacin harin, amma babu wanda ya jikkata a cikinsu.
A ranar Litinin, kwamishinan ‘yan sanda na Abia, Danladi Isa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa harin faru a bangaren jihar Imo.
Ya ce rundunarsa ta aika da rahoton lamarin zuwa rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo domin daukar matakin da ya dace.
Chukwumerije dan marigayi Sanata Uche Chukwumerije ne, wanda ya taba wakiltar jihar a Majalisar Dattawa.
Kokarin da aka yi na tuntubar Chaka ta wayar salula bai yi nasara ba, domin layukan wayarsa ba su shiga ba.
'Dan uwan kwamishinan ya magantu
Amma a wani rubutu da dan uwansa Dike Chukwumerije ya wallafa a Facebook, inda yake alhini kan lamarin, ya tabbatar da harin yana mai cewa:
"Sun tsira daga yunkurin kashe su, duk da cewa motar ta cika da harsashi yayin harin.”
Yan bindiga sun kona mutane a Imo
Kun ji cewa yan bindiga sun tare motoci a kan wani babban titi a jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, sun banka musu wuta.
An ruwaito cewa maharan sun hallaka mutane da dama da suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, sun ƙona wasu a harin.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ɗora alhakin kai harin kan ƙungiyar ƴan aware watau IPOB.
Asali: Legit.ng

