An Yi Babban Rashi a Katsina, Sabon Shugaban Karamar Hukumar Bakori Ya Rasu

An Yi Babban Rashi a Katsina, Sabon Shugaban Karamar Hukumar Bakori Ya Rasu

  • Shugaban karamar hukumar Bakori, Hon. Aminu DanHamidu, ya rasu a ranar Litinin, kasa da watanni uku da rantsar da shi
  • Sanata Shehu Sani da Gwamna Dikko Radda sun bayyana alhinin su tare da tunawa da kyawawan halayen marigayi DanHamidu
  • Yayin da jama'a ke ci gaba da nuna alhinin rasuwar shugaban karamar hukumar, Janare Bature ya ce DanHamidu ya yi rashin lafiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Murnar babbar Sallah ta koma makoki a jihar Katsina, yayin da shugaban karamar hukumar Bakori, Hon. Aminu DanHamidu ya rasu.

Rahotanni sun bayyana cewa, Hon. Aminu DanHamidu ya rasu ne a yammacin ranar Litinin, bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Shugaban karamar hukumar Bindawa a jihar Katsina, Hon. Aminu DanHamidu ya rasu
Shugaban karamar hukumar Bakori, Hon. Aminu DanHamidu da ya rasu. Hoto: @ashehubkr
Source: Instagram

Katsina: Shugaban karamar hukuma ya rasu

Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani, ya tabbatar da rasuwar shugaban karamar hukumar na Bakori a shafinsa na Facebook a ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Ina Katsina, Zamfara?: An taso malaman addini a gaba kan kiran dokar ta ɓaci a Benue

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu Sani ya ce mutuwar Hon Aminu DanHamidu babban rashi ne, yana mai cewa:

"Hon Aminu DanHamidu, shugaban karamar hukumar Bakori:
Allah ya gafarta masa, ya masa sakayya da gidan Aljanna firdausi, Amin.
"Ina mika sakon ta’aziyya ga iyalansa, al’umman Bakori da jama’a da gwamnatin jihar Katsina.
"An yi babban rashi"

Kafar watsa labarai ta Katsina Post, ta tabbatar da rasuwar shugaban karamar hukumar bakori, inda ta rahoto cewa:

"Allah ya yi ma shugaban karamar hukumar Bakori, Hon. Aminu Danhamidu rasuwa.
"Allah ya gafarta mashi, ya kyautata makwancin shi, amin."

Hon. Aminu Danhamidu ya lashe zaben ciyaman

Marigayi Hon. Aminu Danhamidu na daga cikin 'yan takarar kujerar shugaban karamar hukuma na jam'iyyar APC da suka lashe zabe a Fabrairun 2025.

Mun ruwaito cewa jam'iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 34 na jihar Katsina, a zaben da hukumar KASIEC ta gudanar a ranar 15 ga Fabrairu.

A ranar 15 ga watan Afrilu, gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda ya rantsar da zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar ciki har da marigayi Hon. Danhamidu.

Kara karanta wannan

Zambia: Tsohon shugaban ƙasa, Lungu ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 68

Hon. Danhamidu ya yi rashin lafiya

Mai tallafawa gwamnan jihar Katsina, a ma'aikatar harkokin ruwa, Janare Bature, ya shaidawa Legit Hausa cewa:

"Maganarsa wadda ya fadi ta tsaya mani a rai kafin rasuwarsa.
"A lokacin da ake rantsar da su ya yanke jiki ya fadi, aka tafi da shi asibiti. Bayan ya farfado ake ce masa yallabai aka ce ka rasu? Ya yi murmushi ya ce idan kwanana ya kare zan tafi na bar duniyar ba makawa.
"Daga nan ne aka kawoshi gidan gwamnati aka rantsar dashi. Yau gashi ya tafi ya bar duniyar."
Gwamnan jihar Katsina, ya yi alhinin rasuwar shugaban karamar hukumar Bakori
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda. Hoto: @dikko_radda
Source: Facebook

Gwamnatin Katsina ta yi ta'aziyyar DanHamidu

Ibrahim Kaula Mohammed, babban sakataren watsa labaran gwamnan Katsina ya fitar da sanarwar ta'aziyyar rasuwar Hon. DanHamidu.

A cikin sanawar da ya wallafa a shafinsa na Facebok, Ibrahim Kaula ya ce:

"Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana alhinin rasuwar Hon. Aminu Dan Hamidu, shugaban karamar hukumar Bakori, wanda ya rasu a ranar Litinin, 9 ga Yuni, 2025.

Kara karanta wannan

Tsohon mawakin gargajiya a Najeriya ya rasu, Atiku da gwamna Mbah sun yi ta'aziyya

"A cikin saƙon ta’aziyya mai cike da jimami, Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin ɗan jam’iyya na gari, gogaggen ma’aikaci, kuma ɗan siyasar da ya sadaukar da rayuwarsa wajen bauta wa jama’a da gaskiya, tawali’u da ƙwazo."

Ganduje ya kaddamar da yakin zaben Katsina

Tun da fari, mun ruwaito cewa, shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ciyamomi a jihar Katsina.

A yayin taron, Ganduje ya karbi sama da mutane 40,000 da suka sauya sheka zuwa APC daga jam'iyyun adawa ciki har da tsohon shugaban jam'iyyar PDP.

Gwamna Dikko Radda ya yi alƙawarin gudanar da zaɓen shugabannin kananan hukumomi mai inganci, tare da fatan jama'ar Katsina za su zabi jam'iyyar APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com