Yadda 'Yan Ta'addan Boko Haram Suka Farmaki Buratai a Borno
- Ƴan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai farmakin ta'addanci kan wani sansanin sojojin Najeriya da ke garin Buratai
- Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun farmaki sansanon sojojin na Buratai inda suka lalata kayan aiki na sojoji
- Ndume ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da ƙara taɓarɓarewa a sassa daban-daban na ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan sansanin sojojin Najeriya da ke Buratai a jihar Borno.
Harin wanda ake zargin ƴan ta'addan Boko Haram ne suka kai shi, ya ƙara tayar da hankali game da tabarbarewar tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

Source: Facebook
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na Channels Tv a daren ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan Boko Haram suka farmaki Buratai
A cewar Sanata Ali Ndume, ƴan ta'addan sun farmaki sansanin sojojin ne a ranar Juma'a.
Ko da yake ba a fitar da cikakken bayani kan adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba, Sanata Ndume ya bayyana cewa musayar wuta mai tsanani ta ɓarke tsakanin ƴan ta’addan da dakarun da ke Buratai.
“Muna cikin mawuyacin halin tsaro. Kwanaki biyu da suka wuce, an kai wa Buratai hari a wajen sansanin sojoji a Borno."
“Dakarun sun mayar da martani da jarumtaka, amma ƴan ta’addan sun samu damar lalata kayan aikin sojoji masu yawa."
- Sanata Ali Ndume
Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta’addan sun kai farmaki ne kan manyan kayan aiki na sojoji da suka haɗa da motocin MRAPS, manyan bindigogi da kuma tankokin yaƙi.
A wasu lokuta, Ndume ya ƙara da cewa, ba wai kawai suna lalata waɗannan kayan aiki ba ne, har suna kwashe su gaba ɗaya su gudu da su.
"Lamarin tsaro a Borno yana tabarbarewa cikin sauri. Ƴan ta’addan yanzu suna yawo babu tsoro, suna ƙonawa da satar kayan aikin sojoji."
- Sanata Ali Ndume

Source: Twitter
Ali Ndume ya koka kan rashin tsaro
Sanata Ndume ya kuma yi amfani da wannan dama wajen bayyana halin da Najeriya ke ciki gaba ɗaya dangane da tsaro, inda ya ce rikice-rikice, fashi da makami da kuma cin amanar ƙasa sun yaɗu zuwa sassa daban-daban na ƙasar.
“Dukkanin yankuna shida na ƙasar nan suna fama da matsalolin tsaro daban-daban."
“Ko a yankin Kudu maso Kudu, muna fama da satar mai. A wannan lokaci, yankin Kudu maso Yamma ne kadai ke da dan kwanciyar hankali fiye da sauran sassan ƙasar nan."
- Sanata Ali Ndume
Ƴan Boko Haram sun sace malamin addini
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'addan Boko Haran sun yi awon gaba da wani malamin addinin Kirista a jihar Borno.
Ƴan ta'addan sun sace Rabaran Daniel Afina ne bayan sun tare.motar da yake ciki a kan hanyar Gwoza-Limankara.
Tsagerun sun kuma hallaka wani mutum ɗaya tare da yin awon gaba da sauran fasinjojin da ke tafiya tare da shi.
Asali: Legit.ng

