Hajjin Bana: Gwamna Ahmed Ya Gwangwaje Alhazan Sokoto a Saudiyya

Hajjin Bana: Gwamna Ahmed Ya Gwangwaje Alhazan Sokoto a Saudiyya

  • Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya yi wa Alhazan jihar sha tara ta arziƙi a ƙasa mai tsarki watau Saudiyya
  • Ahmed Aliyu ya ba da kyautar kuɗi ga Alhazan yayin da ziyarce su domin taya su murnar kammala aikin Hajjin bana cikin nasara
  • Gwamna Ahmed Aliyu ya kuma buƙace su da su sanya jihar a cikin addu'a domin shawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da take fuskanta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Saudiyya - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ba Alhazan jihar kyautar kuɗi don barka da Sallah.

Gwamna Ahmed ya ba Alhazai 3,200 Riyal 1,000 na Saudiyya, wanda yayi daidai da Naira 450,000 a matsayin kyautar Sallah.

Gwamnan Sokoto ya ba Alhazai kyauta
Gwamnan Sokoto ya ba Alhazai kyautar kudi a Saudiyya Hoto: @Ahmedaliyuskt
Source: Twitter

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin da ya kai ziyara ga Alhazan jihar Sokoto a Minna, inda ya taya su murnar kammala aikin Hajji cikin nasara, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Kisan rashin imani," Magidanci ya halaka matarsa mai tsohon ciki a jihar Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa wannan kyauta na da nufin tallafa musu da kuɗi yayin da suke shirin dawowa gida Najeriya, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Alhazan Sokoto sun samu yabo

Ya nuna jin daɗinsa da yadda Alhazan jihar suka gudanar da kansu, inda ya bayyana cewa babu wanda aka kama yana karya dokokin ƙasar Saudiyya yayin zamansu a ƙasa mai tsarki.

"Ina matuƙar gode muku bisa yadda kuka wakilci jiharmu cikin kima da mutunci a wannan ƙasa mai albarka. Haƙiƙa na yi alfahari da ku."
"Haka kuma ina yaba muku bisa sanin yakamata da ƙwarewa wajen gudanar da ibadar aikin hajji."

- Gwamna Ahmed Aliyu

Ya ƙara tabbatar wa da Alhazan cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen kula da walwalarsu da kuma na sauran mazauna jihar Sokoto.

Gwamna Aliyu ya kuma yabawa Amirul Hajj na jihar, Alhaji Ummarun Kwabo, bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.

Kara karanta wannan

Rufa rufa ta ƙare, Gwamna Alia ya faɗi jiga jigai a Majalisa, Abuja da ke taimaka wa ƴan bindiga

Haka nan ya jinjinawa jami’an hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Sokoto bisa himma da sadaukarwa wajen tsara aikin Hajji mai nagarta.

Gwamna Ahmed Aliyu ya ba Alhazai kyauta
Gwamnan Sokotp ya ba Alhazai kyautar kudi Hoto: @Ahmedaliyuskt
Source: Facebook

Gwamnan Sokoto ya yi kira ga Alhazai

Ya kuma buƙaci Alhazan da su ƙara azama wajen yin addu’o’i domin Najeriya, musamman neman taimakon Allah wajen fuskantar ƙalubalen da ƙasar ke ciki, musamman matsalar tsaro.

“Duk irin ƙoƙarin da muke yi wajen shawo kan matsalar tsaro, addu’a ita ce mafi inganci da makamin da zai kawo ƙarshen wannan matsala da ke hana ci gaban ƙasarmu."

- Gwamna Ahmed Aliyu

Gwamna ya kyauta sosai

Wani mazaunin jihar Sokoto, Mohammed Waziri, ya yaba da matakin da gwamnan ya ɗauka na ba Alhazan kyautar kuɗaɗe.

Ya shaidawa Legit Hausa cewa kuɗin da aka ba su, za su taimaka musu wajen ƙara yin guzuri domin dawowa gida Najeriya.

"Tabbas za su ji daɗin waɗannan kuɗaɗen kuma an taimaka musu domin za su ƙara nauyin lalitarsu."

- Mohammed Waziri

Shugaban NAHCON ya ba Alhazai shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Usman Abdullahi, ya ba da shawara ga Alhazan Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna Alia ya yi magana a ranar Sallah, ya bayyana yadda ƴan bindiga suka kewaye su

Shugaban na NAHCON ya buƙaci Alhazan da su sanya shugabanni cikin addu'o'insu domin su samu damar sauke nauyin da ke kansu.

Ya kuma buƙace su da su yi koyi da ƙasar Saudiyya inda malamai suke tsayawa riƙa yin addu'o'i ga shugabanni domin samun ci gaban ƙasarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng