Kwamishinoni Sun Yi Murabus bayan Sauya Shekar Gwamnan PDP zuwa APC? An Ji Gaskiya
- Sauya sheƙar da Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya yi daga jam'iyyar APC zuwa PDP ya sanya an yaɗa cewa wasu daga cikin kwamishinoninsa sun aje aiki
- Kwamishinonin da aka ce sun ajiye aikin sun fito sun bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikin rahotannin waɗanda aka yaɗa
- Sun bayyana cewa suna nan tare da gwamnan kuma ƙafarsu ƙafar shi wajen ficewa daga jam'iyyar PDP zuwa APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Akwa Ibom - Kwamishinonin jihar Akwa Ibom guda biyu, Farfesa Eno Ibanga da Emem bob da aka ce sun yi murabus daga gwamnatin Gwamna Umo Eno sun yi martani.
Kwamishinonin sun musanta cewa sun sauka daga kujerunsu bayan sauya sheƙar Gwamna Umo Eno daga PDP zuwa jam’iyyar APC.

Source: Facebook
Farfesa Eno Ibanga, cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Evelyn Ibanga, ta fitar, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga gwamnatin Gwamna Eno, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Eno Ibanga (Kwamishinan ayyuka da ma’aikatar kashe gobara) da Emem Bob (Kwamishinan Kudi) sun bayyana cewa suna nan daram tare da gwamnan wajen barin jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.
Gwamna Eno ya fice daga PDP zuwa APC
Gwamna Umo Eno dai ya fice daga PDP zuwa APC tare da yawancin mambobin majalisar zartaswarsa, ƴan majalisar dokoki ta tarayya da ta jiha, da shugabannin ƙananan hukumomi a ranar Juma’a, 6 ga watan Yunin 2025.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, wanda ya kasance cikin gwamnonin APC da suka karɓi Gwamna Eno zuwa jam’iyyar, ya ce sauya sheƙar gwamnan Akwa Ibom zai ƙarfafa APC a yankin Kudu maso Kudu.
Me kwamishinonin suka ce kan yin murabus?
Farfesa Eno Ibanga ya kira rahoton da ke cewa ya yi murabus a matsayin tsantsagwaron ƙarya ce.

Source: Facebook
"Ƙarya ce tsagwaronta wadda wasu masu neman tayar da zaune tsaye suka ƙirƙira da nufin jefa rikici a siyasa da kuma ƙoƙarin ɓata hadin kai da daidaituwar wannan gwamnati."
“Wannan ƙirƙirarren labari ne daga masu yaɗa shi waɗanda nasarar kwamishinan wajen ayyukansa da yin tsayuwar daka wajen biyayyarsa ke damun su."
"A bayyana yake a fili, biyayyar Farfesa Eno Ibanga ga Gwamna Umo Eno da gwamnatinsa tana nan daram, kuma cikakkiya ce ba tare da wata shakka ba."
“Ya ci gaba da aiki tuƙuru domin tallafa wa hangen nesan gwamnan kan ci gaban ababen more rayuwa da kyakkyawan shugabanci a jihar Akwa Ibom."
- Evelyn Ibanga
Kwamishina ya yi murabus a Akwa Ibom
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaya daga cikin kwamishinonin gwamnatin Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya yi murabus daga kan muƙaminsa.
Kwamishinan ayyuka na musamman da tashar jiragen ruwa, Mista Imi Ememobong, ya ajiye muƙaminsa a gwamnatin Gwamna Umo Eno.
Ajiye muƙamin kwamishinan na zuwa ne bayan Gwamna Umo Eno, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Asali: Legit.ng

