'Ina Katsina, Zamfara?: An Taso Malaman Addini a Gaba kan Kiran Dokar Ta Ɓaci a Benue

'Ina Katsina, Zamfara?: An Taso Malaman Addini a Gaba kan Kiran Dokar Ta Ɓaci a Benue

  • Kungiyar 'Pathfinders Arewa Project' ta soki kalaman Rabaran Leonard Kawas na neman a kafa dokar ta baci a jihar Benue saboda rikicin tsaro
  • Shugaban kungiyar, Abdulhamid Abdullahi, ya ce kiran yana da wata manufa ta siyasa domin da bata wa Gwamna Hyacinth Alia suna
  • Shugaban ƙungiyar ya ce rikicin Benue ya samo asali ne daga rikicin filaye da gazawar hukumomi, ba wai yaki ne tsakanin addinai ko wani shiri ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - Kungiyar 'Pathfinders Arewa Project' ta yi watsi da kalaman wasu malamai kan sanya dokar ta-ɓaci a jihar Benue.

Kungiyar ta caccaki Charismatic Bishops Conference of Nigeria (CBCN) kan magana game da matsalar tsaro a jihar Benue.

An caccaki masu kiran sanya dokar ta-ɓaci a Benue
Kungiya ta yi fatali da kiran sanya dokar ta-ɓaci a Benue. Hoto: Legit.
Source: Original

Ana zargin malamai da kiran sanya dokar ta-ɓaci

Kara karanta wannan

'Ka da ku kawo mana maganar Tinubu a 2027': Sheikh ya gargaɗi ƴan uwansa malamai

Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Abdulhamid Abdullahi ya fitar wanda Leadership ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, kungiyar ta gargadi malaman addini da su guji siyasantar da rikicin da ke faruwa a jihar.

Abdullahi ya soki kalaman Rabaran Leonard Kawas da ya zargi wani “shirin Musuluntar da Najeriya” tare da kiran a kafa dokar ta baci a jihar Benue.

Ya kalubalanci wannan kira, yana tambaya me yasa ba a nemi irin wannan mataki a jihohin Zamfara, Katsina da Borno ba duk da yawan kashe-kashen da ake ciki?.

Sanarwar ta ce:

“In ba a kafa dokar ta baci a Zamfara, Katsina ko Borno duk da kashe-kashe da sace mutane ba, me ya sa sai Benue kadai?
“Kalubalen tsaro a Benue na da nasaba da rikicin filaye, lalacewar muhalli da kuma gazawar hukumomi wajen shawo kan rikice-rikice.”
An soki malamai kan kiran dokar ta-ɓaci
Ana ta kiran sanya dokar ta-ɓaci a Benue. Hoto: Hon. Alia Iormem Hyacinth.
Source: Facebook

An gargadi malamai kan siyasantar da tsaro

Abdullahi ya ce kungiyar na jin zafin wadanda rikicin ya shafa, amma danganta matsalar da addini da kabila yana hana gano tushen matsalar da gaske.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista kuma ƙwararren likita, Farfesa Jibril Aminu ya kwanta dama

Ya kara da cewa Najeriya kasa ce mai bin tsarin addini na bai daya, yana mai cewa zargin Musuluntar da kasar ba shi da tushe kuma suna da hatsari sosai.

“Kiristoci da Musulmai duk sun fuskanci matsalolin tsaro a Zamfara, Katsina, Borno da Plateau, mayar da hankali kan Benue kadai yana da wani dalili na siyasa."

- Cewar Abdullahi

Ya ja kunnen malaman addini da su guji zama kayan aiki a hannun ’yan siyasa, yana jaddada rawar da su ke da ita wajen samar da zaman lafiya da warkar da rauni.

Gwamna ya fusata da kiran sanya dokar ta-ɓaci

Kun ji cewa Gwamna Hyacinth Alia na Benue ya yi fatali da masu kiran gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta ɓaci a jihar ganin irin halin da ake ciki a yau.

Gwamna Alia ya ce babu wani dalili da ya kai a ayyana dokar ta ɓaci, ya na mai cewa wasu ƴan siyasa ne ke kokarin fakewa da hakan don cimma burinsu.

Wannan dai na zuwa ke bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ya ɓaci a jihar Ribas, lamarim da ya tada ƙura a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.