Hankula Sun Tashi da Wani Musulmi Ya Mutu a Wani irin yanayi bayan Dawowa daga Idi
- Wani mutum mai shekaru 43 mai suna Kazeem daga unguwar Edun, Ilorin, ya mutu bayan ya fada rijiya bisa shan tabar ‘Colo’
- Lamarin ya faru ne bayan ya dawo daga sallar Idi, ma’aikatan hukumar kashe gobara sun fito da gawarsa daga rijiyar
- Hukumar ta bayyana cewa shan miyagun kwayoyi kamar 'Colorado' yana da hadari, ta bukaci jama’a su guji irin wannan domin kare rayuwarsu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Wani mummunan lamari ya faru a birnin Ilorin da ke jihar Kwara a ranar babbar sallah.
Wani mutum mai shekaru 43 da aka bayyana sunansa da Kazeem ya mutu sanadin fadawa cikin rijiya bayan ya dawo daga sallar idi.

Source: Original
Yadda wani mutum ya mutu a ranar salla
Rahoton Leadership ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a unguwar Edun a Ilorin da ke jihar Kwara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce lamarin ya faru ne sakamakon zargin shan wata kwaya mai suna ‘Colo’ (Colorado) wanda matasa da dama ke amfani da ita.
Majiyoyi sun tattaro cewa lamarin ya faru ne jim kadan bayan Kazeem ya dawo daga sallar Idi a ranar Juma’a.
An gano cewa ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara sun fito da gawar Kazeem daga cikin rijiyar gidan domin sanin halin da yake ciki.

Source: Facebook
An tsamo gawar mutumin a cikin rijiya
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Hassan Adekunle, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.
Ya ce ma’aikatan hukumar sun garzaya wurin bayan sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 10:29 na safiyar Juma’a cewa wani ya fada rijiya a unguwar Alapo, Edun, Ilorin.
Ya ce:
“An samu kiran gaggawa daga dakin karbar bayanan hukumar kashe gobara da misalin karfe 10:29 cewa wani mutum ya fada rijiya.
"Nan da nan aka tura ma’aikata zuwa wurin, inda suka fito da gawar daga rijiyar.
“Wanda lamarin ya faru da shi, Kazeem, an ce ya fada rijiyar ne saboda shan wata kwaya mai suna Colo (Colorado) jim kadan bayan sallar Idi.
“An mika gawar ga sufeta Babatunde Amos na ofishin ‘C’ Division na ‘yan sanda da ke Ilorin."
Hukumomi sun shawarci al'ummar Kwara
Ma’aikatar na jiran iyalan mamacin su bayyana don karbar gawar dan uwan nasu, cewar rahoton The Guardian.
Daraktan hukumar a jihar, Prince Falade Olumuyiwa, ya shawarci jama’ar jihar da su guji shan miyagun kwayoyi, yana cewa irin hakan na janyo rashin ɗa'a da kuma mutuwa.
Yan bindiga sun hallaka jami'an yan sanda
Kun ji cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari wurin hakar ma’adinai a Oreke-Oke-Igbo, jihar Kwara, inda suka kashe ’yan sanda biyu.
Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa an kashe ASP Haruna Watsai da sufeta Tukur Ogah bayan sace wani dan kasar waje ƙasa da mutum daya.
Kakakin jami'an ’yan sanda ya ce kwamishinansu rundunar ya sha alwashin ceto waɗanda aka sace tare da cafke waɗanda suka aikata laifin.
Asali: Legit.ng

