'Ka da Ku Kawo Mana Maganar Tinubu a 2027': Sheikh Ya Gargaɗi Ƴan Uwansa Malamai
- Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu, yana mai cewa a bar batun sake zabensa a 2027 saboda halin kunci
- A cewarsa, mutane na cikin mawuyacin hali, ya kuma gargadi malamai da 'yan siyasa da ka da su kawo maganar Tinubu a cikin al'umma
- Malamin ya ce ya janye goyon baya daga gwamnatin, yana rokon Allah SWT ya dauki ran shugabannin da ke haddasa matsala a kasar nan
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Fitaccen malamin Musulunci, Alkali Abubakar Salihu Zaria ya yi magana kan salon mulkin Bola Tinubu.
Malamin Musuluncin ya caccaki gwamnatin inda ya ce ko kusa bai kamata ana maganar Tinubu a zaben 2027.

Source: Facebook
Alkali Abubakar Salihu Zaria ya caccaki Tinubu
Malamin ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da Saleem Yusuf Muhammad ya wallafa a Facebook a jiya Juma'a 6 ga watan Yunin 2025.

Kara karanta wannan
'Goron sallar Tinubu ce': A ƙarshe, Gwamna ya jero dalilansa na komawa jam'iyyar APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon Sheikh ya gargadi malamai da yan siyasa da su guji kawo tallar Tinubu a zaben 2027 da ke tafe.
Ya ce mutane suna cikin wani irin mummunan yanayi saboda mulkin kunci da ake ciki a yanzu wanda ya sanya al'umma dawowa daga rakiyar Tinubu.
"Malamai ga sako na gare ku ina muku nasiha ku kama bakunanku, ka da wani yazo mana da maganar wannan mutumin.
"Ita ce magana ta gaskiya don Allah a bar maganar wannan mutumin, kowa ya sani babu wanda ya isa ya ce a kafuwar wannan gwamnati ya ce babu ni a ciki.
"Amma maganar wannan mutumin a yi hakuri haka, a yi hakuri haka, a yi hakuri ba mu da bukatarsa.
- Cewar Alkali Abubakar Salihu Zaria

Source: Facebook
Gudunmawar Shehin a zaben Tinubu a 2027
Sheikh Alkali Abubakar Salihu ya ce yana daya daga cikin wadanda suka goyi bayan gwamnatin amma yanzu ya janye.
Ya ce mutane da dama su ma sun yi fatali da salon mulkin Tinubu saboda halin kunci da yan kasar ke ciki na tsadar rayuwa.
A cewarsa:
"Lokacin da muke zaton za a yi mana adalci ai mu muka ce a yi shi, to yanzu ni na fita, ban sani ba ko ku kuna ciki."
Addu'o'in da malamin ya yi kan zaben 2027
Daga bisani, Sheikh ya yi addu'o'i ga azzaluman shugabanni da kuma malamai da za su zama matsala a kasa.
Malamin ya roki Allah ya dauki ran wadanda za su zama matsala a kasar cikinsu har da 'yan siyasa da malaman addini.
Sheikh ya fadi matsayarsa kan zaben Muslim/Muslim
A baya, kun ji cewa malamin Musulunci, Alkali Abubakar Salihu Zaria ya bayyana matsayarsa kan zaben tikitin Musulmi da Musulmi ba da ake ta ce-ce-ku-ce.
Malamin ya bayyana cewa ko kadan bai yi nadamar zaben Bola Tinubu a tsarin Musulmi da Musulmi ba duba da yadda ake caccakar gwamnatin.
Sheikh Salihu ya ce ko kadan ba tsarin Musulmi da Musulmi ba ne ya kawo damuwar da ake ciki inda ya ce daga Allah ne.
Asali: Legit.ng
