Malabu: Mohammed Abacha Ya Garzaya Kotun Koli kan Mallakar Rijiyar Mai
- Mohammed Sani Abacha ya fara kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara kan mallakar rijiyar mai ta OPL 245
- Kamfanin Malabu Oil and Gas ya kai kara kotun koli kan lasisin rijiyar man dake hannun kamfanin Agip and Shell
- Da fari, kotun daukaka kara ta soke hukuncin da ke goyon bayan Malabu, ta ce an shigar da ƙara bayan lokaci ya kure
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja – Mohammed Abacha, ɗan marigayi tsohon shugaban mulkin soja, Sani Abacha, ya fara shirin kalubalantar hukuncin da ya shafi mallakar kamfanin Malabu Oil and Gas.
Yana kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ta yi watsi da ƙoƙarinsa na dawo da mallakar rijiyar man OPL 245.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa lauyoyinsa, ƙarƙashin Reuben Atabo, sun shigar da buƙatar neman izini a gaban kotun daukaka kara. Sun nemi kotun ta ba su dama su daukaka kara zuwa kotun koli kan hukuncin da aka yanke a ranar 23 ga Mayu.

Kara karanta wannan
Haka Allah ya so: Martanin Sarkin Gwandu da kotu ta tabbatar da tsige shi daga sarauta
Kamfanin Malabu ya shigar da ƙarar Abacha a kotu
The Cable ta wallafa cewa kamfanin Malabu Oil and Gas ya shigar da ƙara a babbar kotun tarayya yana kalubalantar yadda aka sake raba lasisin hakar mai (OPL 245) ga kamfanonin Agip da Shell.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar lauyoyin Agip, ƙarƙashin Babatunde Fagbohunlu, ta shigar da ƙorafi kan hurumin kotun tarayya bisa dalilai da dama.

Source: UGC
Daga cikin dalilan har da cewa ƙarar ta zo da jinkirin fiye da shekaru biyar bayan bayar da lasisin da ake takaddama a kai.
A ranar 22 ga Disamba, 2020, kotun da ke sauraron ƙarar ta yi watsi da ƙorafin farko da Agip ta shigar kan karar Malabu.
Malabu: An soke hukuncin kotun daukaka kara
A hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ranar 23 ga Mayu, 2025, wani kwamitin alkalai uku ya soke hukuncin da kotun tarayya ta yanke.
Hamma Akawu Barka, wanda ya jagoranci kwamitin alkalai, ya ce kotun ƙasa ba ta magance muhimman batutuwan da Agip ta kawo ba.
Kotun ta amince da korafin Agip tare da yanke hukunci cewa ƙarar da Malabu Oil ta shigar a kotun tarayya ya wuce wa’adin watanni uku da doka ta kayyade.
Saboda haka, kotun daukaka kara ta soke hukuncin kotun tarayya da Mai shari’a Binta Nyako ta yanke.
Iyalan Abacha sun yi martani ga IBB
A baya, kun ji 'ya'yan marigayi Janar Sani Abacha sun yi martani kan kalaman da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya yi game da mahaifinsu.
A cikin littafin A Journey in Service, IBB ya bayyana cewa yana da nadamar soke zaben 12 ga Yuni, 1993, wanda ya bayyana cewa MKO Abiola ne ya lashe shi.
Sai dai ya ce dalilin soke zaben ba daga gare shi kadai ya fito ba, illa wata manufa ce da Abacha da mukarrabansa suka jagoranta, ba tare da ya san za a yi haka ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
