Rikicin Sarauta: Yadda Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II Suka Yi Sallar Idi a Kano
- Duk da rikicin sarauta da ake fama da shi a Kano, musulmi sun yi idin sallar layya cikin zaman lafiya da lumana yau Juma'a, 6 ga watan Yuni
- Sarki na 15, Aminu Ado Bayero da na 16, Khalipha Muhammadu Sanusi II sun yi sallah a filayen idi daban-daban
- Manyan jami'an gwamnatin Kano ciki har da mataimakin gwamna, kwamishinoni da hakimai sun halarci filin idin da Sanusi ya yi limanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - A yau Juma’a, mazauna Kano sun bi sahun sauran Musulmai a fadin duniya wajen gudanar da sallar Eid-el-Kabir, watau sallar layya ta bana 2025.
Sarakunan Kano na 15 da na 16, Alhaji Aminu Ado Bayero da Khalifa Muhammadu Sanusi II, sun yi sallar idi a wurare daban-daban a cikin birnin Kano.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi Ii ya yi tattaki da ƙafa na sama da kilomita 1 ranar Sallah a Kano, an ji dalili

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Aminu Ado Bayero, wanda aka tube daga mulki amma daga baya aka mayar da shi bisa umarnin kotu mai cike da ruɗani, ya yi sallar idi a fadar Nasarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Aminu Ado ya yi sallar idi a Kano
Sarkin Malamai, Malam Kamalu Inuwa, shi ne ya yi limanci a masallacin idin fadar Nasarawa, ya ja hankalin musulmi su yi koyi da sadaukarwar Annabi Ibrahim (AS).
Limamin ya ja hankalin Musulmai da su kasance masu hakuri, nuna wa juna soyayya, da juriya, tare da tsayuwa kan ibada da kyawawan halaye.
Sanusi II ya yi limancin sallar idi a Kofar Mata
A ɗaya ɓangaren, Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II, wanda gwamnatin jihar Kano ta mayar kan mulki, ya jagoranci dubban Musulmai a filin idi na Kofar Mata.
Manyan jami’an gwamnati, ciki har da Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, da kwamishinoni, hakimai da masu rike da sarauta sun halarci filin idin da Sanusi II ya yi limanci.
Bayan kammala sallah, Sarki Sanusi II ya yi huduba, inda ya buƙaci jama’a su goyi bayan hukumomin tsaro wajen yaki da tabarbarewar tsaro da karuwar tashin hankali a tsakanin matasa.
Huɗubar da Muhammadu Sanusi II ya yi
"Ya kamata mu haɗa kai mu kawo karshen tashe-tashen hankula musamman ƴan daba, wannan aiki ne da ya rataya a kan kowa, bai kamata mu bari a lalata zaman lafiyar da muka gada daga kakanninmu ba."
- Sanusi II.
Muhammadu Sanusi II ya jaddada muhimmancin tarbiyya da kulawar iyaye, yana mai cewa kyakkyawan tarbiyya na farawa ne daga gida.
"Iyaye su kula da tarbiyyar 'ya'yansu, su kare su daga fadawa cikin miyagun ayyuka, domin su zama mutanen kirki masu tarbiyya da bin doka da oda," in ji shi.

Source: Twitter
Duk da cewa ana fama da rikicin sarauta tsakanin ɓangarori biyu, rahotanni sun nuna cewa an yi idi cikin lumana a faɗin birnin Kano.
Sanusi Isiya, wani mazaunkin Kano ya tabbatar wa wakilin Legit Hausa cewa an yi sallah cikin kwanciyar hankali.
Sai dai ya koka kan abin da ya danganta da rashin adalci, hana Sanusi II yin hawan sallah karo na biyu kenan a jere.
"Mu kam Alhamdulillah, an yi sallah lafiya amma dai ba mu ji daɗin yadda ake hana sarki hawa ba, al'ada ce da muka taso muka gani ana yi, amma sallah biyu kenan ba a yi ba a Kano," in ji shi.
Sarki Sanusi ya janye hawan sallaha a Kano
A wani labarin, kun ji cewa Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya soke hawan Sallah da ya fara shirin yi a jihar.
Sarki Sanusi II ya soke hawan ne domin gujewa tashin hankula da bai wa al'umma damar gudanar da shagulgulan sallah cikin zaman lafiya.
Tun da farko, Sarkin ya umarci dukkan Hakimai da su hallara a fada ranar Laraba, 4 ga watan Yuni, 2025 don fara shirin gudanar da Hawan Sallah.
Asali: Legit.ng

