Magana Ta Kare, Sarki Sanusi II Ya Canza Shawara kan Batun Hawan Sallah a Kano
- Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya soke hawan sallah da ya fara shirin yi a jihar saboda masalahar jama'a
- Sanusi II ya bayyana haka ne a daren jiya Alhamis, 5 ga watan Yuni, 2025 bayan tattaunawa da wakilan gwamnatin jihar Kano
- Hakan dai na zuwa ne bayan rundunar ƴan sanda ta sake jaddada cewa dokar da ta ƙaƙaba ta haramta hawan sallah tana nan daram
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Bayan dogon nazari da shawarwari, Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya soke hawan Sallah da ya fara shirin yi a jihar.
Sarki Sanusi II ya soke hawan ne domin gujewa tashin hankula da bai wa al'umma damar gudanar da shagulgulan sallah cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Source: Twitter
Mai martaba Sarkin ya sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a daren jiya Alhamis, 5 ga watan Yuni, 2025, kamar yadda Leadership ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarki Sanusi II ya haƙura da hawan sallah
Da yake jawabi a fadarsa da ke ƙofar Kudu ranar jajibirin sallah, Muhammadu Sanusi ya ce ya soke hawan sallah ne domin guje wa tayar da zaune tsaye da fargaba.
Sarki Sanusi II ya kuma bayyana cewa an ɗauki mataki sokewar ne biyo bayan tuntubar juna da tattaunawa tsakanin Majalisar Sarakunan Kano da Gwamnatin Jihar Kano.
Ya jaddada cewa masarauta ta haƙura da yin hawan sallah saboda maslahar jama'a tare da tabbatar da cewa al'umma sun yi bukukuwan Sallah cikin salama.
Abin da ya jawo hana hawan Sallah a Kano
Tun da farko, Sarkin ya umarci dukkan Hakimai da su hallara a fada ranar Laraba, 4 ga watan Yuni, 2025 don fara shirin gudanar da Hawan Sallah.
Sai dai rundunar ‘yan sandan Kano ta sake jaddada dokar haramta hawan sallah da duk wani nau'i na hawan doki saboda barazanar tsaro, rahoton Tribune.
Rundunar ta kara da cewa har yanzu akwai barazanar tsaron da ta ss aka hana hawan sallah a lokacin karamar sallah, don haka ta ce dokar haramcin tana nan daram.

Source: Facebook
Sanusi ya bukaci jama'a su fito sallar Juma'a
A yayin jawabin nasa, Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga jama’a da su halarci duka Sallar Idi da ta Juma’a, yana mai cewa wannan zai ba mutum lada mai yawa.
Ya kuma gargadi jama’a kada su dogara da wasu fatawowi da ke cewa idan an yi Sallar Idi, ba sai an yi ta Juma’a ba, yana mai cewa irin wadannan ra’ayoyi ba su isa su zama hujja wajen barin wajibcin Juma’a ba.
"Mu bi tafarkin da zai fi dacewa da addini da zaman lafiya. Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya mu yi sallah lafiya," in ji Sarkin.
Aminu Ado ya soke hawan sallah
A ɗaya ɓangaren, kun ji cewa sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya dakatar da shirin hawan sallah a lokacin shagulgulan babbar sallah.
Wannan matakin na zuwa ne sakamakon tattaunawa da hukumomin tsaro da kuma duba halin da ake ciki a jihar Kano da kasa baki daya.
Masarautar Kano ɓangaren Aminu Ado ta bayyana cewa ana bukatar jama’a su rungumi zaman lafiya da biyayya ga doka fiye da komai a lokutan sallah.
Asali: Legit.ng


