Hajjin 2025: Mahajjaci Ɗan Najeriya Ya Rasu a Wuri Mai Daraja da Albarka a Saudiyya

Hajjin 2025: Mahajjaci Ɗan Najeriya Ya Rasu a Wuri Mai Daraja da Albarka a Saudiyya

  • Najeriya ta ƙara rasa mahajjaci ɗaya a wurin tsayuwar Arafah a ƙasar Saudiyya yayin aikin hajjin bana 2025
  • Shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya tabbatar da rasuwar mahajjacin ga manema labarai bayan kammala addu'ar ƙasa
  • Fitaccen malamin ya kuma musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa mahajjacin ya rasu ne sakamakon tsananin zafin rana a ranar Arafah

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Wani mahajjaci daga Najeriya wanda har kawo yanzu ba a bayyana sunansa ba, ya rasu a Arafah a kasar Saudiyya.

Hukumar kula da alhazai ta ƙasa watau NAHCON ta tabbatar da rasuwar mahajjacin ga manema labarai.

Mahajjata sun mamaye dutsen Arafah.
Mahajjaci daga Najeriya ya kwanta dama a ranar Arafah Hoto: @Haramain
Source: Getty Images

Najeriya ta rasa mahajjaci 1 a filin Arafah

Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana cewa wani ɗan Najeriya ya rasu a filin Arafah yayin gudanar da ibadar Hajji ta bana, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Hanyar samun tsira da abubuwan da limamin Arafa ya bayyanawa Musulmai

Farfesa Abdullahi Saleh ya bayyana hakan ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala addu’ar ƙasa da hukumar NAHCON ta shirya a Arafah.

“Mun samu labari mara daɗi cewa mun rasa ɗaya daga cikin mahajjatanmu a yau a Arafah. Mun kuma rasa wani kafin mu bar Makkah,” in ji shi.

Ɗan Najeriya ya rasu saboda zafin rana a Rafah?

Farfesa Abdullahi wanda aka fi sani da Abdullahi Pakistan, ya karyata raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa tsananin zafin rana da aka yi a ranar Arafah ne ya yi ajalin mahajjacin.

Shugaban NAHCON, wanda babban malamin addinin musulunci ne a Najeriya, ya ce mahajjacin ya rasu ne yadda kowa ke rasuwa idan lokacinsa ya yi, amma ba sanadin zafin rana ba.

Idan baku manta ba, hukumomin Saudiyya sun gargaɗi mahajjata da su gujewa hawa dutsen Arafah daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma saboda tsananin zafin rana.

Yadda alhazai suka yi hawan Arafah a aikin hajjin 2025.
Hukumar NAHCON ta musanta zargin cewa zafin rana ne ya yi ajalin mahajjacin Hoto: Getty Image
Source: Getty Images

Mahajjata sun kaucewa gargaɗin Saudiyya

Kara karanta wannan

Yadda mahajjata suka take gargaɗin minista game da hawa dutsen Arafah a Saudiyya

Ministan Hajji ya ce zafin ranar zai iya jawo wa mutane ciwo, yana mai ba mahajjata shawarar su zauna a tantunansu, su yi ibada, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Sai dai Legit Hausa ta rahoto cewa dubban mahajjata ciki har da ƴan Najeriya sun yi fatali da wannan gargaɗi, inda suka hau dutsen Arafah duk da zafin ranar da ake yi.

Wannan ne ya sa bayan samun labarin rasuwar mahajjacin, mutane suka fara yaɗa cewa ya rasu ne sakamakon tsakanin zafin rana, lamarin da NAHCON ta musanta.

A wani muhimmin tanadi, NAHCON ta sake jaddada cewa ba za a bayyana sunan mamacin ba, har sai an sanar da iyalansa kamar yadda doka ta tanada.

Mahajjaci daga Kano ya rasu a Makkah

A wani labarin, kun ji cewa wani mahajjaci daga jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, ya rasu a birnin Makkah, kasa da sa’o’i 24 kafin hawa Arafaha a hajjin bana.

Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutumin ga manema labarai, ta ce lafiya kalau suka baro gida da marigayin.

Ta kara da cewa Shu'aibu na fama gyambon ciki da hawan jini sama-sama, amma likitocin Saudiyya sun ce bugun zuciya ne ya yi ajalinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262