Ba Sauki: Sojoji Sun Hallaka Manyan Kwamandojin ISWAP a Borno
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kan ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP yayin wani artabu da suka yi a jihar Borno
- Sojojin sun hallaka kwamandojin ƙungiyar guda uku bayan sun kawo hari a Mallam Fatori da ke ƙaramar hukumar Abadam
- Hakazalika, jami'an tsaron sun hallaka wasu ƙarin ƴan ta'adda 12 tare da ƙwato makamai a yayin arangamar da suka yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai, sun hallaka wasu kwamandojin ƙungiyar ISWAP guda uku a Borno.
Dakarun sojojin sun hallaka kwamandojin ne yayin wani hari da ƴan ta'addan suka kai a Mallam Fatori, ƙaramar hukumar Abadam ta jihar Borno.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP
Sojojin sun samu nasarar ne bayan sun samu goyon baya daga ɓangaren sama na rundunar.
Majiyoyi masu sahihanci sun bayyana cewa kwamandojin da aka kashe sun haɗa da Amir Abu Ali Weldone, Amir Ibunu, da Amir Abu Waldume.
An kashe kwamandojin ne a lokacin musayar wuta mai tsanani da ta ɗauki awa huɗu a sansanin ƴan gudun hijira da ke Mallam Fatori.
A cewar majiyoyin, waɗannan kwamandoji da aka kashe suna taka muhimmiyar rawa a tsarin ayyukan ƙungiyar ISWAP.
Ana ganin cewa Abu Ali Weldone ne ke jagorantar ayyukan ta’addanci a yankin Kerenoa da ke kusa da iyakar Najeriya da Nijar.
Majiyoyin sun tabbatar da cewa ƴan ta'addan sun ƙaddamar da harin daga yankin Kaniram da safiyar ranar Laraba, inda suka kai hari ga sansanin sojoji.
Sun yi gungu wajen kawo harin, tare da amfani da jirage marasa matuƙa masu ɗauke da makamai da manyan makamai kamar bindigogin AGL.
Sai dai sojojin ƙasa waɗanda suka riƙa amfani da ƙananan bama-bamai da tankuna, sun samu nasarar daƙile harin.
Sojojin sun samu nasarar daƙile harin bayan musayar wuta mai tsanani, inda suka tilastawa maharan janyewa cikin ruɗani.

Source: Original
An kashe wasu ƴan ta'adda
Aƙalla ƴan ta’adda 12 ne aka tabbatar da kashe su, tare da ƙwato bindigogin AK-47 guda bakwai, manyan bindigogin GPMG guda uku, rokokin RPG guda biyu, da wasu abubuwan fashewa da dama.
Majiyoyin sun ƙara da cewa ana ci gaba da yin bincike da kimanta ɓarnar da aka yi, amma kashe waɗannan kwamandojin guda uku babbar nasara ce ga sojoji.
Sojoji sun yi bajinta
Faisal Sulaiman ya shaidawa Legit Hausa cewa dakarun sojojin na Najeriya sun nuna bajinta wajen hallaka ƴan ta'addan.
"Tabbas wannan abin a yaba ne nasarar da dakarun sojojin suka samu. Muna fatan za su ci gaba da kakkaɓe ƴan ta'addan."
"Allah ya ƙara musu ƙwarin gwiwar ci gaba da fatattakar ƴan ta'addan a cikin daji."
- Faisal Sulaiman
Sojoji sun hallaka ƴan ta'addan ISWAP
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan ƴan ta'addan ISWAP/Boko Haram a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun samu nasarar ne bayan sun daƙile wani hari da ƴan ta'addan suka kai a garin Damboa.
Sojojin sun samu goyon baya daga jiragen yaƙi na sojojin sama a yayin musayar wutar da suka yi da ƴan ta'addan ta tsawon lokaci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


