Bayan Jita Jita na Yawo, Wike Ya Magantu kan Masu Juya Akalar Gwamnatin Tinubu

Bayan Jita Jita na Yawo, Wike Ya Magantu kan Masu Juya Akalar Gwamnatin Tinubu

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan zargin cewa wasu na juya akalar gwamnatin Shugaban kasa, Bola Tinubu
  • Wike ya yabawa Tinubu kan cire tallafin mai, yana cewa waɗanda ke cin moriyar damfara da tallafin za su ci gaba da yi da bai cire ba
  • Ya ce Najeriya na da matsaloli da dama amma za ta iya samun ci gaba idan an kafa tsarin shugabanci nagari da haɗin kan 'yan kasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya magantu kan zargin juya akalar gwamnatin Bola Tinubu.

Wike ya musanta zargin cewa akwai wasu mutane masu ƙarfi da ke juya mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Wike ya magantu kan masu juya gwamnatin Tinubu
Wike ya ƙaryata cewa ana juya gwamnatin Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nyesom Ezenwo Wike.
Source: Facebook

Wike ya caccaki masu yiwa Tinubu sharri

Channels TV ta ce Wike, lauya kuma tsohon gwamnan Rivers ya fadi haka a jawabinsa a taro da aka yi a Ile-Ife da ke jihar Osun.

Kara karanta wannan

'Yan kwadago sun yi wa Tinubu wankin babban bargo bayan cika shekara 2 a mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan Rivers ya yi mamakin mutane yadda suke yada jita-jita hankali kwance ba tare da tantancewa ba.

Ya ce:

“Ya nuna jarumta, a ƙarƙashin Tinubu, babu wani abu wai masu juya gwamnati, wannan shugaban ne ke da ikon mulki."

Ministan ya ce dukkanin shugabannin Najeriya na baya ciki har da Obasanjo da Jonathan, ba su da ƙarfin halin cire tallafin man fetur.

Wike ya yabawa salon mulkin Tinubu
Wike ya jinjinawa Tinubu kan cire tallafin mai. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike.
Source: Facebook

Wike ya yabi Tinubu kan cire tallafin mai

Wike ya ce da Tinubu bai cire tallafin ba, mutane da yawa za su ci gaba da amfana daga damfarar tallafin man fetur.

Ya ce duk da cewa Najeriya ba ta tabuka komai ba a shekaru 60 da suka wuce, har yanzu tana iya yin fice da shugabanci nagari.

Wike ya ce dole ne a gina amana da haɗin kai tsakanin ‘yan kasa don a samu ci gaba da daidaito a Najeriya, cewar rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Wike ya tono sirrin gwamnonin PDP, ya fadi alfarmar Tinubu da suke nema

Ya ce:

“Najeriya da muke buri ba za ta sauko daga sama ba, tana buƙatar hangen nesa, sadaukarwa da aiki tuƙuru daga kowa.”

Nyesom Wike ya yi mamakin masu sukarsa

Wike ya soki masu cewa bai dace da matsayin minista ba, yana mai cewa akwai matsala da mutanen da ke faɗin haka.

Ya ce waɗanda ke bin bashin hayan kudin kasa a Abuja dole su biya, inda ya ce sama ba za ta fāɗi ba idan sun biya hakkin gwamnati.

Taron ya samu halartar Ooni na Ife, Oba Enitan Ogunwusi; Ministan Kuɗi, Wale Edun; da tsofaffin gwamnoni Ifeanyi Ugwuanyi da Samuel Ortom.

Wike ya damu da 'butulcin' Fubara

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kuma yin magana game da rigimarsa da dakataccen Gwamna Siminalayi Fubara a Rivers.

Wike ya ce yana kuka duk lokacin da ya tuna yadda Fubara ya ci amanarsa duk da taimakon da ya yi masa a siyasa wanda ya yi sanadin zama gwamna a jihar.

Tsohon gwamnan Rivers ya ce shi ya dauki nauyin Fubara, ya ba shi abinci da goyon baya, amma daga baya ya zama mai taya abokan gabansa aiki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.