Tsohon Minista kuma Ƙwararren Likita, Farfesa Jibril Aminu Ya Kwanta Dama

Tsohon Minista kuma Ƙwararren Likita, Farfesa Jibril Aminu Ya Kwanta Dama

  • Tsohon Ministan ilimi da na harkokin man fetur, Farfesa Jubril Aminu, ya rasu yana da shekaru 85 a Abuja bayan fama da jinya
  • Zai yi jana’iza da misalin karfe 2:00 na rana a Masallacin Abuja kafin a kai gawarsa Yola, daga nan zuwa karamar hukumar Song
  • Farfesa Aminu ya yi aiki a matsayin Jakadan Najeriya a Amurka, Sanata da Minista, kuma ya shugabanci tarukan kungiyar OPEC

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - Rahotanni sun tabbatar da rasuwar tsohon Ministan ilimi da man fetur, Farfesa Jubril Aminu, ya rasu.

Aminu, tsohon jakada kuma kwararren likita ya mutu yana da shekaru 85 a duniya.

Tsohon minista a Najeriya ya bar duniya
An sanar da rasuwar Farfesa Jibril Aminu. Hoto: El-yakub Abubakar.
Source: Facebook

Jibril Aminu ya riga mu gidan gaskiya

Hakan na daga cikin wata sanarwa da tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Barau ya yi jimamin rasuwar yan wasan Kano, ya mika tallafin N22m ga iyalansu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu majiyoyi sun nuna cewa dattijon ya rasu a yau Alhamis a Abuja bayan doguwar rashin lafiya.

A cewar majiyar, za a yi masa sallar jana’iza da karfe 2:00 na rana a Masallacin Abuja a yau, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Bayan haka, za a dauki gawarsa zuwa Yola sannan daga nan zuwa karamar hukumar Song a jihar Adamawa.

Farfesa Aminu likita ne na zuciya, ya kammala karatun likitanci a Jami’ar Ibadan a 1965, inda ya fi kowa hazaka, cewar Daily Post.

Ya yi aiki da Najeriya a mukamai da dama kamar Jakada a Amurka (1999–2003) Sanatan Adamawa (2003–2011), da Minista (1989–1992).

Marigayin yayin da ya riƙe muƙamin Ministan Man Fetur, ya zama Shugaban Kungiyar Masu Fetur ta Afirka a 1991 da kuma Shugaban OPEC (1991–1992).

Haka kuma, ya kasance wakili a taron tsara kundin tsarin mulki na kasa a tsakanin 1994 zuwa 1995.

Kara karanta wannan

Sanata ya fadi yadda ake kara karfin Boko Haram don dagula mulkin Tinubu

Shehu Sani ya yi alhinin rasuwar Jibril Aminu
Shehu Sani ya fadi gudunmawar da Jibril Aminu ya ba al'umma. Hoto: Shehu Sani.
Source: Twitter

Shehu Sani ya yi alhinin rasuwar Jibril Aminu

Shehu Sani ya ce a matsayinsa na Ministan Ilimi, ya aiwatar da muhimman gyare-gyare.

Ya ce tabbas kasa ta rasa ɗaya daga cikin manyan masana da masu hangen nesa inda ya yi addu'ar Allah ya jikansa, ya sa ya huta a Aljanna Firdausi.

"Na samu labarin rasuwar Farfesa Jibril Aminu cikin bakin ciki, Tsohon Shugaban Jami'a ne, Ministan Ilimi, daga baya kuma Ministan Man Fetur, ya kuma kasance Sanata da ya wakilci jihar Adamawa.
"A lokacin da yake Ministan Man Fetur, shi ne ya gina matatar mai ta Eleme da rumbunan ajiya na man fetur a fadin ƙasa.
"Tun bayan barinsa, ba a ƙara wata ba har yanzu. Ya gudanar da sauye-sauye masu yawa a cikin NNPC."

- Cewar Shehu Sani

Tsohon babban alkalin kotu ya rasu

A baya, kun ji cewa an sanar da rasuwar tsohon alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja bayan fama da jinya yana da shekaru 79 a duniya.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Wata mahajjaciya daga Najeriya ta sake rasuwa a asibitin Makkah

Majiyoyi daga kotun sun ce marigayi Daniel Dantshoho Abutu ya rasu kamar a jiya Laraba 4 ga watan Yunin 2025.

Marigayin Abutu ya shugabanci kotun daga Satumba 2009 zuwa Maris 2011, kotun ta ce ya yi aiki da gaskiya, rikon amana da jajircewa da yake alkalanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.