Musulmi Zai Iya Cin Bashi Ya Sayi Ragon Layya da Sallah? Babban Limamin LASU Ya Yi Bayani
- Babban limamin jami'ar LASU, Farfesa Amidu Sanni ya shawarci Musulmi su gujewa cin bashi don sayen dabbar layya da babbar sallah
- Malamin ya ce duk wanda bai da sararin yin layya, to wajibcin ya faɗi a kansa, yana mai cewa bai kamata mutane su jefa kansu a matsala ba
- Sanni ya bukaci shugabanni tun daga Bola Tinubu har ciyamomin kananan hukumomi su yi duk mai yiwuwa wajen saukakawa talakawa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Babban Limamin Jami’ar Jihar Legas (LASU), Farfesa Amidu Sanni, ya gargaɗi Musulmi da su guji karɓar bashi domin cika wajibcin ibadar Layya a Sallah.
Babban malamin addinin musuluncin ya yi wannan kira ne a sakon barka da babbar sallah da ya fitar yau Alhamis, 5 ga watan Yuni, 2025 a jihar Legas.

Source: Getty Images
Farfesa Sanni ya ja kunnen Musulmai da kada su jefa kansu cikin ayyukan haram ko almubazzaranci don kawai kwaɗayin ladan layya, The Nation ta rahoto.
Malamin ya taya 'yan Najeriya murnar zagayowar babbar sallah, inda ya yi addu’ar zaman lafiya da dawowar alhazai lafiya daga aikin Hajji.
Shin musulmi zai iya cin bashi ya yi layya?
Amidu Sanni ya bayyana cewa duk wanda ba shi da halin sayen dabbar da ta halatta a yi layya da ita, an ɗauke masa wajibci.
Malamin, wanda ya duba halin matsin tattalin arzikin da Najeriya ke ciki, ya ce:
"Wanda bai da ikon sayen dabbar layya, an ɗauke masa. Don haka, babu dalilin da zai sa mutum ya je ya ci bashi ko ya shiga mu'amala ta haram don ya yi layya.”
“Babbar Sallah ta bana ta zo a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru biyu da kafa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda hakan yana da muhimmanci ga rayuwar ‘yan Najeriya.”

Kara karanta wannan
Gwamna Bago ya bi sahun ƴan sandan Kano, ya hana hawan Sallah saboda abin da ya faru
Malamin ya ja hankalin shugabannin Najeriya
Farfesa Sanni ya yi kira ga shugaban ƙasa, gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi da su dauki matakin ceto ‘yan Najeriya daga halin kuncin da suke ciki.
“Shirin ‘sabunta fata’ na gwamnatin Tinubu na iya cimma nasara idan aka mayar da hankali wajen aiwatar da manufofin da suka shafi jin daɗin talaka, domin rage radadin cire tallafin mai da kuma faduwar darajar Naira.
“Aiwatar da mafi ƙarancin albashi na ƙasa yadda ya kamata zai taimaka matuƙa wajen kwantar da hankalin jama’a," in ji shi.

Source: Getty Images
Farfesan ya kuma yi tsokaci kan yadda jama’a suka mayar da martani kan kudirin tilasta kada kuri’a da aka soke kwanan nan, yana mai cewa talakawa sun faɗi ra'ayoyinsu.
Ya shawarci shugabanni da su rika sauraron irin waɗannan ra’ayoyi daga jama’a yayin da suke ƙoƙarin ɗaukar matakai nan gaba, kamar yadda Leadership ta kawo.
Sarkin musulmi ya ja hankali kan ranar Arafah
A wani rahoton, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci musulmi su yi amfani da ranar Arafah wajen neman Allah ya kawo sauƙi a Najeriya.

Kara karanta wannan
Yadda aka zabga wa Sarki lafiyayyen mari a taron da gwamnan Ondo ya kaddamar da titi
Ya bayyana cewa addu’o’in da za a yi a wannan rana za su iya jawo rahamar Allah da kuma mafita ga matsalolin da ƙasa ke fuskanta.
Baya ga haka, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce yin azumi a wannan rana yana share zunuban da suka gabata da kuma na gaba idan Allah ya yarda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
