Mutuwa Rigar Kowa: Tsohon Babban Alƙalin Kotun Tarayya Ya Bar Duniya
- An shiga jimami da aka sanar da rasuwar tsohon alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja bayan fama da jinya yana da shekaru 79 a duniya
- Marigayi Daniel Dantshoho Abutu ya rasu kamar yadda magatakarda na kotun, Sulaiman Hassan, ya tabbatar a cikin wata sanarwa
- Abutu ya shugabanci kotun daga Satumba 2009 zuwa Maris 2011, kotun ta ce ya yi aiki da gaskiya, rikon amana da jajircewa da yake alkali
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja ta yi rashin tsohon alkalinta da ya ba da gudunmawa sosai.
An ce marigayi Daniel Dantshoho Abutu, wanda ya riƙe shugabancin babbar kotun tarayya, ya rasu bayan ya sha fama da jinya.

Source: Facebook
Tsohon alkalin babbar kotun ya kwanta dama
Magatakardan babbar kotun tarayya, Sulaiman Hassan shi ya bayyana rasuwar Abutu cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abutu ya kasance shugaban kotun daga watan Satumba na shekarar 2009 zuwa Maris 2011 wanda aka kwatanta lokacinsa da cewa ya ba da gudunmawa mai tsoka.
Hassan ya bayyana marigayi alkalin kotun a matsayin alkalin da ya yi aiki da girmamawa, gaskiya da jajircewa wajen samar da adalci.

Source: Getty Images
Wane umarni kotun ta bayan kan rasuwar?
Har ila yau, Kotun ta umarci sanya hotonsa a fili a kowane rassa tare da bude rajistar ta’aziyya.
Ya ce:
“Babbar kotun tarayya na bakin ciki da sanar da rasuwar tsohon shugabanmu, Mai shari’a D. D. Abutu, wanda ya yi aiki da ƙwazo da gaskiya.
“Don girmama gagarumar gudunmawar da ya bayar, dukkan rassan kotun su sanya hoton marigayin a wuri mai kima da kuma girmamawa.”
Hassan ya ce kotun ta umarci bude rajistar ta’aziyya a dukkan rassanta don ba alkalan, ma’aikata, lauyoyi da jama’a damar yin ta’aziyya.
Ya kara da cewa za a fitar da ƙarin bayani kan shirye-shiryen jana’izarsa nan ba da jimawa ba domin birne shi a kan lokaci, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Musulmi sun yi babban rashi, Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
Karanta wasu labarai masu alaƙa da wannan:
- Rai Baƙon Duniya: Daga Nada Shi Alkalin Kotu, Mai Shari'a Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- An Dakatar da Manyan Alkalan Najeriya 3, Za Su Rasa Albashin Wata 12
- Alkalin Babbar Kotun Jihar Kwara, Oyinloye, Ya Rasu Yana da Shekara 58
- Daga karshe, Kotu Ta Yi Zama kan Shari'ar Kisan Gilla da Aka Yi Wa Janar Alkali a Jos
Babban alkalin kotu a Najeriya ya rasu
A baya, kun ji cewa majiyoyi sun tabbatar da cewa Allah ya karbi ran babban alkalin Ekiti, Mai shari'a Oyewole Adeyeye bayan fama da rashin lafiya.
Duk da cewa ba a samu cikakken bayani game da rasuwar ba, amma majiyoyi sun shaida cewa alkalin ya rasu ne a safiyar Talata 5 ga watan Nuwambar 2024.
A shekarar 2023 da ta gabata ne aka ruwaito cewa ginin babbar kotun jihar ya rufta kan marigayin a lokacin da ya ke aiki cikin ofishinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
