Saura Kiris a Fara Ibadar Hajji, Alhajin Kano Ya Kwanta Dama a Saudiyya

Saura Kiris a Fara Ibadar Hajji, Alhajin Kano Ya Kwanta Dama a Saudiyya

  • Wani mahajjaci daga jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, ya rasu a birnin Makkah, kasa da sa’o’i 24 kafin fara ayyukan hajji
  • Shu'aibu wanda manomi ne daga ƙaramar hukumar Bebeji, ya rasu ne sakamakon bugun zuciya bayan gajeriyar jinya
  • Duk da guda daga cikin yan uwansa dake tare da shi ya tabbatar da cewa lafiya kalau suka bar Kano, amma ajali ya yi kira

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Ƙasa da sa’o’i 24 kafin a fara manyan ayyukan hajji na bana, wani mahajjaci daga jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, ya rasu a birnin Makkah da ke ƙasar Saudiyya.

Mai magana da yawun hukumar kula da alhazan Jihar Kano, Malam Suleiman Dederi, ne ya tabbatar da rasuwar Sgu'aibu Jibrin ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Gwamna ya karrama jami'in NIS da ya ki karbar N10m wajen bokan da aka kama

Ana dab da fara aikin hajjin bana
Alhajin Kano ya rasu a Saudiyya Hoto: Inside The Haramain
Source: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa bayanai sun nuna cewa mamacin ya rasu ne a wani asibiti a Saudiyya bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhajin Kano ya rasu a kasar Saudiyya

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa daya daga cikin ‘yan uwansa marigayin, Sama’uddin Aliyu Kadawa, wanda shi ma yana cikin mahajjatan bana, ya tabbatar da rasuwar.

Ya shaidawa manema labarai a birnin Makkah cewa kafin su baro Kano, Shu'aibu yana fama da cutar gyambon da hawan jini sama sama, amma baya ga wannan lafiya lau suka isa kasa mai tsarki.

Sama'uddin Aliyu ya kara da cewa sai bayan sun isa Saudiyya ne, rana guda kafin rasuwar dan uwansa aka same shi da cutar da ta yi ajalinsa.

Saudiyya: Asalin Alhajin Kano da ya rasu

A cewar Sama’uddin, marigayin manomi ne daga ƙauyen Gargai da ke cikin ƙaramar hukumar Bebeji a jihar Kano.

Ya bayyana cewa sun san Shu'aibu da gyambon ciki da hawan jini, amma likitocin Saudiyya sun ce ya samu bugun zuciya ne, wanda ya yi ajalinsa.

Kara karanta wannan

DSS da sojoji sun tarfa yaran 'dan ta'adda, sun aika mayakan Dogo Gide 45 barzahu

Alhajin Kano ya rasu bayan jinya
Shu'aibu Jibrin ya yi fama da bugun zuciya a Saudiyya Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ya ce:

“Ya fita lafiya daga gida, daga baya ne ya fara rashin lafiya, aka kwantar da shi a Asibitin Sarki Abdulazeez na Saudiyya. Bayan kwana biyu, aka sallame shi saboda ya samu sauki."
“Amma jiya sai yanayinsa ya ƙara dagulewa, aka sake garzaya da shi asibiti. Duk da ƙoƙarin da likitocin Najeriya da na Saudiyya suka yi, ya rasu da misalin 2.50 na safe."

Gwamnan Kano ya duba abincin alhazai

A baya, mun wallafa cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar bazata zuwa babban dakin girki da ke kula da abincin mahajjatan jihar a birnin Makka.

Ziyarar ta gudana ne a daren Lahadi, yayin da mahajjatan ke shirin tafiya Mina domin ci gaba da ibada, kuma gwamnan ya duba yanayin abincin da ake dafa wa alhazan.

Ya kuma duba kayan ciye-ciye da 'ya'yan itatuwa kamar tuffa, lemu da ruwan kwalba da ake bai wa mahajjatan, ya kuma ya ɗibi abincin da kansa domin tabbatar da ingancin girkin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng