Gwandu: Bayan Shekaru 20, Kotun Ƙoli Ta Raba Gardama kan Rigimar Sarauta

Gwandu: Bayan Shekaru 20, Kotun Ƙoli Ta Raba Gardama kan Rigimar Sarauta

  • Kotun Koli ta kawo ƙarshen rigimar sarautar Gwandu da ta shafe shekaru 20, an ki dawo da Mustapha Jokolo kan karaga
  • Alkalin kotun ya ce kotun jihar Kebbi ba ta da hurumin sauraron karar da Jokolo ya shigar ba tare da bin ka’ida ba
  • Kotun ta ce ba a bi matakin shigar da ƙara zuwa ga gwamna ba kafin zuwa kotu, don haka hukuncin bai da tushe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbi - Kotun Koli a ranar Laraba ta kawo ƙarshen rikicin shari’ar sarautar Gwandu da ke jihar Kebbi da ake yi tsawon shekaru 20.

Kotun yayin hukuncinta, ta soke dawowar Al-Mustapha Haruna Jokolo a matsayin Sarkin Gwandu.

Kotun Koli ta raba gardama kan sarautar Gwandu
Kotun Koli ta tabbatar da Muhammadu Ilyasu-Bashar a matsayin Sarkin Gwandu. Hoto: Surajo Muhammad.
Source: Facebook

Gwandu: Kotu ta kalubalanci hukuncin da aka yi

A hukuncin da Mai Shari'a, Emmanuel Agim ya karanta, ya ta ce Kotun Jihar Kebbi ba ta da hurumin sauraron karar da Jokolo ya shigar, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Ondo: Kotu ta raba gardama kan shari'ar da ke neman tsige gwamnan APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta ce, bisa dokar Sarakuna ta Jihar Kebbi, sai wanda ke da ƙorafi ya fara kai saƙo ga gwamna kafin ya je kotu.

Sanarwar ta ce:

“An shigar da wannan ƙara da wuri, ba tare da an kai ƙorafi ga gwamna ba. Don haka kotun ba ta da hurumi."

Yaushe Jokolo ya rasa kujerar sarautar Gwandu

Jokolo ya rasa sarauta a shekarar 2005, amma Kotun Jihar Kebbi ta dawo da shi a 2014, kuma kotun daukaka ƙara ta goyi bayansa a 2016.

Sai dai Gwamnatin Kebbi da Sarkin yanzu, Alhaji Muhammadu Ilyasu-Bashar, sun garzaya Kotun Koli don kalubalantar hukuncin da aka yi.

Kotun Koli ta amince da karar su, tana mai cewa kotunan ƙasa sun ci karo da doka da suka ci gaba da sauraren shari’ar ba bisa ka’ida ba.

Mai Shari'a Agim ya ƙara da cewa:

“Gazawar sanar da gwamna ta hana kotu hurumin sauraron ƙarar wanda ya sa aka soke hukuncin kotunan ƙasa."

Kara karanta wannan

DSS da sojoji sun tarfa yaran 'dan ta'adda, sun aika mayakan Dogo Gide 45 barzahu

Kotu ta kawo karshen rigimar sarauta a Gwandu
Kotu ta raba gardama kan rigimar sarauta a Gwandu. Hoto: Legit.
Source: Original

Hukuncin kotu kan rigimar sarautar Gwandu

Saboda haka Kotun Koli ta soke duka hukuncin kotun jiha da na daukaka ƙara, tana tabbatar da cewa Jokolo ba zai dawo sarauta ba.

Sai dai a hukuncin ƙin yarda da matakin, Mai Shari'a, Ibrahim Mohammed Salami ya ce kotunan sun yi daidai, inda ya goyi bayan dawowar Jokolo.

Ya jaddada cewa dole ne gwamna ya bi doka da adalci wajen shawo kan batutuwan da suka shafi nadin sarauta a jiharsa, cewar Daily Post.

An tsara hukuncin ranar 6 ga Yuni, amma aka gaggauta shi zuwa 4 ga Yuni saboda hutun babbar sallah da ke tafe a kasar.

Sarautu a Najeriya da tasirinsu

A Najeriya, sarakunan gargajiya suna da taka muhimmiyar rawa wajen zaman lafiya, ci gaban al’umma, da kare al’adun gargajiya.

Duk da cewa ba su da ikon mulki kai tsaye a tsarin dimokuraɗiyya, suna da tasiri sosai a zukatan mutane, musamman a yankunan karkara.

Kara karanta wannan

Gombe: Bayan kashe babban 'dan sanda a Kano, yan kalare sun tasamma hallaka DPO

Sarakuna su ne jigo wajen sasanta rikice-rikicen cikin gida, wanzar da zaman lafiya da kuma ba da shawarwari ga shugabannin siyasa.

Yadda siyasa ta sauya sarautar gargajiya

Sai dai a ‘yan shekarun nan, ana kara samun matsin lamba daga wasu ‘yan siyasa masu muradin dagula tsarin sarauta domin cimma muradunsu.

A lokuta da dama, ana amfani da nadin sarauta a matsayin wata hanya ta siyasa, inda gwamnoni ke sauke ko nada sarakuna bisa dalilan da ke da nasaba da ra’ayin siyasa, ba bisa cancanta ko ra’ayin al’umma ba.

Wannan hali ya kawo ruɗani da rikice-rikice da suka shafi masarautu da dama, kamar yadda aka gani a rikicin sarautar Gwandu.

Hakan yana nuni da yadda siyasa ke kutse a harkar da ya kamata ta kasance bisa al’ada da martaba.

Idan ba a sanya idanu ba, wannan zai ci gaba da rugujewa martabar sarauta a Najeriya, kuma hakan na iya janyo tabarbarewar tsarin zamantakewa da al’adu.

Sarkin Bunza a Kebbi ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Bunza a jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya, Dr. Mustapha Muhammad Bunza ya riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Gwandu: Rikicin dawo da Sarki kan mulki ya zo ƙarshe, Kotun Koli za ta yanke hukunci

'Dan majalisar wakilai, Hon. Ibrahim Mohammed ya nuna alhininsa kan rasuwar basaraken inda ya ce ya ba da gudunmawa.

Marigayin ya yi mulki na tsawon shekaru 30 yana kare al’adu da ci gaban yankin Bunza, tare da ba da shawarwari ga mutane da dama

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.