Ana Jimamin Iftala'in Ambaliyar Ruwa, Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke a Neja
- Makiyaya da manoma sun ba hammata iska a ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya ta Najeriya
- Rikicin wanda ya ɓarke a tsakanin Fulani da manoma na ƙabilar Gwari, ya auku ne bayan zargin shiga gona ba bisa ƙa'ida da yin ɓarna
- An samu asarar rai sakamakon ɓarkewar rikicin yayin da wasu mutane daga ɓangarorin biyu suka samu raunuka daban-daban
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Niger - An samu ɓarkewar mummunan rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar Neja.
Aƙalla mutum ɗaya ya rasa ransa, wasu da dama kuma sun jikkata sakamakon rikici tsakanin makiyaya Fulani da manoman Gwari a ƙauyen Kpowi, gundumar Fuka, cikin ƙaramar hukumar Munya.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana haka a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Bayan ganawa da wakilan gwamnati, ma'aikatan shari'a sun amince a janye yajin aiki
Yadda rikicin manoma da makiyaya ya ɓarke a Neja
Rikicin wanda ya faru a ranar 2 ga watan Yuni da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, ya samo asali ne daga gardama kan zargin shiga gona ba bisa ƙa’ida ba da kuma lalata amfanin gona.
Rigimar ta rikiɗe zuwa rikici mai tsanani tsakanin mambobin ƙabilun Fulani da Gwari.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa mutum shida daga ɓangaren Fulani, da suka haɗa da Ahmadu Bature, Dauda Bello, Haruna Umaru, Shuaibu Bature, Bature Bello, da Safiya Auta, sun samu raunuka daban-daban.
Haka zalika, mutane huɗu daga ɓangaren ƙabilar Gwari, Yusuf Pada, Pius Pada, Dantala Yusuf, da Joshua Mai’anguwa, suma sun ji rauni a yayin arangamar.
Dukkan waɗanda suka jikkata an garzaya da su zuwa asibitin gwamnati da ke Kaffin-Koro domin samun kulawar likita.
Sai dai an tabbatar da rasuwar Ahmadu Bature a lokacin da aka kai shi asibitin.
Hukumomi sun shiga cikin lamarin
An shawo kan lamarin bayan saurin shigowar jami’an tsaro, kuma an gayyaci shugabannin duka ɓangarorin biyu domin gudanar da tattaunawar zaman lafiya.
Rikici tsakanin manoma da makiyaya na jawo asarar rayuka da dukiya a tsakanin ɓangarorin guda biyu.
Mafi yawan lokuta rikicin na samo asali bisa zargin barin dabbobi su shiga gonakin manoma su yi musu ɓarna.
Matsalar rikicin manoma da makiyaya ta daɗe tana faruwa a sassa daban-daban na Najeriya.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan rikicin manoma da makiyaya
- Rikicin manoma da makiyaya ya ɓarƙe a Taraba, an samu asarar rayuka
- Gombe: An rasa rayuka a rikicin makiyaya da manoma, an kona amfanin gona
- Fadan Fulani da makiyaya ya barke a Jigawa, an samu asarar rayuka
Sanata ya ba da tallafi kan ambaliya a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Neja ta Arewa, Abubakar Sani Bello, ya ba da tallafi kan ambaliyar ruwan da aka yi a garin Mokwa, wadda ta jawo asarar rayukan mutane da lalata gidaje.
Sanatan wanda shi ne kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ƙasashen waje, ya ba da tallafin N50m don rage raɗaɗi ga mutanen da lamarin ya shafa.
Abubakar Sani Bello ya kuma miƙa saƙpn ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon iftila'in na ambaliyar ruwa.
Asali: Legit.ng
