NCC Ta Ba Bankuna Sabon Umarni kan Cire Kudin Amfani da Tsarin USSD
- Hukumar sadarwa ta kasa (NCC) ta dakatar da cire kudin amfani da wayar hannu don hada-hada, wato USSD daga asusun banki
- Ana ganin NCC ta dauki matakin ne domin kawo karshen koken kamfanonin sadarwa na cewa bankuna na hana su hakkinsu
- Bankin UBA ya tabbatar wa kwastomomi cewa sabon tsarin ya fara aiki, tare da bayani kan yadda za a ci gaba da mu’amala ta USSD
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar sadarwa ta kasa (NCC) ta umarci bankuna da su dakatar da cire kudin tsarin amfani da waya don hada hada, wato USSD kai tsaye daga asusun abokan huldarsu.
A cewar wata sanarwa da bankin UBA ya aika ga abokan cinikayyarsa a ranar Talata, ya ce a za a rika cire kudin ne daga layin wayar hannunsu, ba daga asusun banki ba.

Kara karanta wannan
'Tun a tafiya motarmu ke samun matsala,' Yar wasan Kano ta fadi 'dalilin' hadarinsu

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa wasu bankuna sun fara bin umarnin, inda UBA ya ce sabon tsarin ya fara aiki daga ranar Talata, 3 ga Yuni, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bankuna sun fara bin umarnin hukumar NCC
Punch ta wallafa cewa wannan sabon umarni na iya zama wani yunkuri daga NCC don warware rikicin biyan kudin USSD da ke tsakanin kamfanonin sadarwa da bankuna.
UBA ya shawarci abokan huldarsa da su ci gaba da amfani da sauran hanyoyin bankin zamani da tsarin intanet don samun saukin gudanar da hada-hada.
Sanarwar bankin ta ce:
"Dangane da umarnin da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta bayar, ku sani cewa daga ranar 3 ga Yuni, 2025, ba za a kara cire kudin ayyukan bankin USSD daga asusun bankinku ba."
"A maimakon haka, za a rika cire kudin daga katin wayarku, kamar yadda tsarin NCC na tanada.:
NCC: Bankin UBA ya fitar da sabon tsari
A karkashin sabon tsarin biyan kudin, UBA ya bayyana cewa kowace mu’amala ta USSD za ta ciri ₦6.98 a cikin kowane daƙiƙa 120, wanda kamfanin sadarwa ne zai cire daga kudin kiran waya.
Ya ce:
"Za a rika samun sako na neman amincewarka a duk lokacin da za a yi amfani da USSD, sannan za a cire kudin ne kawai idan ka amince da hakan."
"Idan baka son ci gaba da amfani da USSD a karkashin wannan sabon tsarin ba, za ka iya dakatar da amfani da tashar USSD din gaba daya."

Source: UGC
A watan Disamba 2024, Babban Bankin Najeriya (CBN) tare da NCC sun ba da umarni ga kamfanonin sadarwa da bankuna da su warware rikicin bashin Naira biliyan 250 na kudin USSD.
Kamfanonin sadarwa sun so dakatar da sabis saboda bashin da bankuna suka ci, wanda ya jawo NCC ta shiga tsakani domin tabbatar da an samu fahimtar juna.
NCC ta amince da karin kudin kira
A baya, kun ji cewa hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da bukatar kamfanonin sadarwa na ƙara kuɗin kira da sauran ayyukan sadarwa a kasar nan.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: 'Yan daba sun farmaki kamfanin simintin a Gombe, an kashe mutum 1
Wannan mataki yana zuwa ne sakamakon karin farashin kayayyaki da hauhawar kudin aiki da kamfanonin ke fuskanta, kamar yadda suka yi korafi.
Rahotanni sun nuna cewa kamfanonin sadarwa sun shafe watanni suna koka wa kan matsin tattalin arziki da karin kudin da suke fuskanta wajen gudanar da ayyukansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
